Saboda haka kamfanin NNPC ya shawarci 'yan Najeriya da su daina ribibin sayen man irin na fargaba, don kuwa akwai isashen man.
Rundunar kawancen kasashen yankin tafkin Tchadin ta kaddamar sabon farmaki da zummar kammala kakkabe sauran burbushin mayakan ISWAP da BOKO HARAM a yankin tafkin Tchadin.
‘Yan bindiga sun kafa sansanoninsu akan tsaunukan dake zagaye da babban birnin, daga inda kuma suke kaddamar da hare-hare akan mutanen da basu san hawa ba balle sauka a garuruwan dake wajen birnin.
A ci gaba da yakin da take da ‘ƴan kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas, rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta ce tayi nasarar ceto mata shida daga hannun ‘ƴan Boko Haram bayan barin wuta da sojoji a dajin Sambisa.
Biyo bayan karuwar aika aikar 'yan bindigar da ke satar mutane a wasu yankunan babban birnin Tarayyar Najeriya, Ministan birnin ya nuna damuwa da takai ga har ya kira wani taron gaggawa kan tsaro da manyan kusoshin tsaron babban birnin.
Yayin da zabukan fidda gwani ke kara matsowa a Najeriya, rigingimun cikin gida a jam'iyyar APC mai mulkin kar sai kara daukar sabon salo ya ke yi.
Rundunar tsaron Najeriya tace jiragen yakinta sun hallaka wasu yan fashin daji a jihar Katsina tare da kubutar da wasu mutanen da akai garkuwa dasu a daidai lokacin da tsaron ke kara sukurkucewa a jihar Kaduna.
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce ta gano wani shirin boye na tada rikici a wasu yankunan kasar, musamman ma dai yankin arewa ta tsakiyar kasar, inda kuma ake son yin amfani da addini da kabilanci wajen sake wani sabon rikicin ta hanyar ingiza daukar fansa.
A Wani matakin kara tunkarar matsalolin tsaro a Najeriya, babban hafsan hafsoshin sojojin kasar, Laftanar Janaral Farouk Yahaya na can na gudanar da wani gagarumin taro da baki dayan manyan kwamandojin rundunonin sojin kasar.
Attoni Janar na Tarayya kuma ministan Shari'a Abubakar Malami ya mikawa Shugabar babbar kotun Tarayya takardar bukatar neman mikawa Amurkan DCP Abba Kyarin don fuskantar shari'a dangane da batun taka rawa a damfarar da ake zargin Hushpuppy da aikatawa.
Wata Babbar kotun Tarayya a Abuja taki amincewa da bukatar beli da tsohon kwamandan rundunar Aiki Da cikawa ta IRT, DCP Abba Kyari ya nemi kotun ta bashi.
Kungiyar kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ta nuna rashin jin dadi dangane da yadda sojojin kasar Mali suka ba kansu wa'adin mulki na shekara biyar kafin su maida kasar bisa tafarkin dimokradiyya.
Tuni kuma hukumar kula da ayyukan ‘yan sandan ta aikewa da sufeto janar na ‘yan sanda wannan mataki da hukumar ta dauka
A ci gaba da kokarin kawo karshen aika aikar yan bindiga dadi a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya, hedkwatar tsaron kasar tace dakarunta dake aiki a karkashin rundunar OPERATION HADIN KAI na ci gaba da ragargazar yan ta'addan dake ta kashe mutane ba gaira ba dalili.
Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriyar wato NAPTIP tace jami'anta tare da hadin gwiwar ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, ofishin jakadancin Najeriya dake birnin New Delhi a kasar Indiya, da kuma ‘yan sandan birnin na New Delhi sun kwato wadansu mata da aka yi safarar su daga Najeriya.
Yanzu dai ta tabbata cewa akwai sabon kyakkyawan fata ga ‘yan Najeriya dake son zuwa Amurka ganin yadda ofishin jakadancin Amurka ya ce zai kara bubbude kofofinsa wajen baiwa ‘yan Najeriya takardun izinin shiga kasar wato Visa
Babban Hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriya, Janaral Lucky Irabor ya ce hadin kai tsakanin mayakan kasashen biyu na da tarin alfanu musamman wajen tunkarar kalubalen tsaro irin na zamani da ke faruwa.
Domin Kari