Tun ma dai gabanin babban taron jam'iyyar ta yi ta fuskantar rigingimu a rassanta na jihohi irin su Kano, kebbi, Bauchi, Ogun da sauransu.
Amma a cewar shugaban jam'iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, kodayake yasan Kano na da matukar muhimmanci maras misaltuwa a wurinsu, bai cika son yin magana akan ricikin jihar ba, amma dai ya san manya sun shigo cikin maganar kuma in Allah ya yarda za a sasanta, kuma haka jihar kebbi ma da sauran jihohin.
To amma Duk da haka rigingimun cikin gidan jam'iyyar na kara damalmalewa a wasu jihohi irinsu Kebbi, musamman ma tun bayan kammala babban taron. Wani fitaccen dan jam'iyyar APC a jihar, Alhaji Zaidu Bala ya yi takaicin yadda 'yan jam'iyyar ke ta komawa Jam'iyyar PDP.
Ya ce kawo yanzu jam'iyyar ta dare gida biyu a jihar, inda ake da bangaren gwamnan jihar Sanata Atiku Bagudu da na tsohon gwamna Sanata Adamu Aleiro, inda tuni jiga jigai daga bangaren Aleiron ke ta canza sheka zuwa PDP.
Da yake tsokaci kan matsalar, malamin kimiyyar siyasa a jami'ar Abuja, Dr. Abubakar Umar Kari ya ce lallai wannan yawan canza sheka Abu ne da ba makawa sai ya faru duba da yadda zabe ke kara durfafowa.
Ya ce wadanda ke canza shekar, kodai wadanda ke da muradin yin takara ne ko kuma wadanda ke son ci gaba da samun damar fada a aji a jam'iyyar ne da a halin yanzu ke fusksntar barazana, don haka basu da wani zabi illa su fice daga jam'iyyar.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: