Lauyoyin Abba kyarin tun farko sun shaidawa kotun cewa, wanda suke karewa yana fama da matsanancin ciwon sugar da kuma hawan jini
Don haka bisa la'akari da wannan su ka nemi kotun ta amince da bukatar neman belinsa.
Sai dai lauyoyin hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato NDLEA sun yi adawa da bukatar inda suka nuna fargabar wanda ake karar ka iya yin katsalandan da shaidu.
Tun farko dai hukumar ta NDLEA ta nemi kotun data bata damar tsare Abba karin na makonni biyu don zurfafa bincike.
Da yake yanke hukunci akan batun, Mai Shari'a Eyang Ekwo yayi watsi da bukatar belin, maimakon haka ya nemi a rika bashi cikakken kulawa da lafiyarsa a inda ake tsare dashi.
Kotun ta sanya ranar goma sha biyar ga watan maris za a dawo don ci gaba da sauraron shari'ar.