Shugaban kwamitin sa ido kan rikita rikitar siyasar da ke addabar kasashen yankin da kungiyar ta ECOWAS ta kafa, kuma tsohon shugaban Najeriya Dr. Goodluck Ebele Jonathan ne ya bayyana haka a wani taro da kwamitin ya yi.
Dr. Goodluck Jonathan ya ce ko da yake ECOWAS ba ta so ta ga ana juyin mulki, in har ba makawa hakan ta faru to bai dace a dauki dogon lokaci ba tare da an maida mulki ga halastacciyyar gwamnatin farar hula ba.
“Ko a shekarar 2012 da sojoji suka yi juyin mulki a Mali, a cikin shekara daya da rabi suka tsara maida kasar bisa turbar dimokradiyya, amma yanzu sojojin kasar na maganar rike kasar har tsawon shekara biyar, abin ko kadan bai dace ba," a cewar Jonathan.
Kwararre kan sha'anin diflomasiyya Ambasada Sulayman Dahiru da ke zama
tsohon jakadan Najeriya a kasashen Sudan da Pakistan, ya ce in bera da sata to daddawa ma na da wari domin mulki ana yi ne don jama'a, kuma lokacin da shugabannin ke kauce hanya ECOWAS ba ta cewa komai sai sojoji sun yi kutse kuma a yi ta tada jijiyar wuya.
Ambasada Dahiru ya nemi ECOWAS da ta dinga bibiyar yadda kasashe mambobinta ke gudanar da mulki kuma duk inda aka sami akasi to ta hanzarta daukar matakan gyara don a gudu tare a tsira tare.
Shi ma masanin harkokin tsaro Air Commodore Baba Gamawa ya koka akan halin da kasar Mali ta shiga, ya nemi sojojin kasar su gaggauta gyara kurakuren da suke cewa ‘yan siyasa sun tafka da nufin maida kasar bisa tsarin dimokradiyya.
Wasu Kasashen Yammacin Afirka dai na fama da matsalolin tsaro da ma rashin kwanciyar hankalin siyasa. A halin da ake ciki, Mali, Guinea Bisau da Burkina Faso na cikin halin tsaka mai wuya a siyasance da ma ta fannin tsaro yayin da ‘yan ta'adda kuma ke kara samun gindin zama a wasu sauran kasashen yankin.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.