Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cire Najeriya A Jerin Kasashen Dake Fuskantar Barazanar 'Yan Fashin Teku A Duniya


Wadansu da ake tunanin 'yan fashi teku ne da aka kama a tekun Lagos
Wadansu da ake tunanin 'yan fashi teku ne da aka kama a tekun Lagos

Hukumar sufurin ruwa ta duniya wato International Maritime Bureau ta cire sunan Najeriya daga jerin kasashen dake fuskantar barazanar 'yan fashin teku a duniya, al'amarin dake nuna irin kyautatuwar sha'anin tsaro a Ruwan kasar,

Babban Hafsan Hafsoshin rundunar mayakan Ruwan Najeriyar Vice Admiral Auwal Zubairu Gambo ya k bayyana haka yayin da yake jawabi wajen bikin cika shekara sittin da shida da kafa rundunar ruwan.

Admiral AZ Gambo wanda babban hafsa mai kula da manufofi da tsare tsare a hedkwatar sojin ruwan kasar Rear Admiral Sa'idu Sulyman Garba ya wakilce shi yace makasudin samun wannan ci gaba shine ganin yadda aka sami raguwa sosai na irin fashin tekun da a baya ake tayi ba kakkutawa, kuma koda ma an sami wani akasi to irin dan abin nanne da ba a rasa ba.

Admiral Gambo yace a a baki dayan shekarar da ta gabata, sau biyu ne kacal akai yunkurin tafka fashi a ruwan Najeriya da shima din bai nasara ba.

Jirgen ruwa a cikin teku
Jirgen ruwa a cikin teku

Yace rundunar mayakan ruwan Najeriya ta yi ta kaddamar da sintiri iri iri wajen ganin ta tsare ruwan kasarnan, yana mai cewa sintirin operation dakatar da barawo shine na karshe da har yanzu ake yinsa wanda yai nasar cafke wasu da ake zargi

Ciki har da cafke wasu mutane 45 da ake zargi an kuma rufe matatun mai da aka samar ba bisa ka'ida har guda dari da saba'in da bakwai kana an rusa tankokin mai na adana man shima ba bisa ka'ida ba sama da dari bakwai.

Bugu da kari an kuma cafke litar mai milyan goma sha daya da aka tace ba bisa ka'ida ba da ake da zummar fitar dashi ketare kana da wani milyan 20 na gurbataccen mai da sauran karin albarkatun man da kudinsu ya kai Naira Biliyan goma sha biyar.

A baya dai hukumomin kasa da kasa sun sanya sunan Najeriya cikin jerin kasashen da ba a aminta da su wajen matsalar tsaro.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG