Da ya ke wa Muryar Amurka karin bayani kan taron, babban mai taimakawa Ministan Abujan kan harkokin yada labarai, Alhaji Abubakar Sani ya ce a taron gaggawan da ministan ya kira da manyan jami'an tsaron, ministan ya jaddada masu bukatar kara sa ido kan irin matsalolin dake karuwa na satar mutane dama aikata miyagun laifuka a birnin.
Jami'an tsaron, kazalika, sun tabbatar wa Ministan cewa suna kara daukar sabbin matakai da tsare tsare da kuma zama cikin shirin ko ta kwana a birnin Abuja da kuma sauran yankunan karkarar babban birnin don tabbatar da tsare rayuka da dukiyar jama'a.
A cewar masanin tsaro, Dr. Kabiru Adamu akwai bukatar daukar wasu muhimman matakai guda uku daga bangaren ministan na tabbatar da tsarin tsaro da zai hada duka bangarorin tsaro, sannan da kuma tattara bayanai da tantancewa wanda keda nasaba da yadda za a shigo da jama'a cikin shirin, don akwai gibi a nan, inda ko a makon da ya gabata saida aka sami zanga zanga a yankin Kuje saboda ta'azzarar matsalar tsaro saboda satar mutane a yankin.
Dr. Kabiru Adamu ya ce akwai kuma bukatar hukumar Birnin Tarayya ta kara hada kai da jihohin da ke makwabtaka da birnin, sannan a tabbatar da sa ido akan hukumomin da ke da alhakin samar da tsaro a birnin ba wai kawai a rinka daukar kudi ana ba su haka sakaka ba.
A yan kwanakinnan dai matsalar tsaro musamman ma satar mutane na karuwa a yankunan babban birnin, inda ko a makon da ya gabata sai da 'yan bindiga suka bindige shugaban kungiyar miyetti Allah kana su ka yi awon gaba da wasu mukarrabansa, abin ma kenan da ya sa wasu 'yan asalin birnin, irinsu Alhaji Ibrahim Tungan Maje ke kira ga Ministan Abujan da ya shigo da 'yan sa kai cikin harkar samar da tsaro a kuma taimaka masu kamar dai yadda abin yake a jihohin dake makwabtaka da birnin
Taron dai ya sami halartar kwamishinan 'Yan sandan birnin, Daraktan Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS, Kwamandan Rundunar Tsaron Fararen Hula ta C NB da dai sauransu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: