Biyo bayan kara tabarbarewar tsaro akan hanyar Abuja zuwa Kaduna, Sufeto Janar Na 'Yansandan Najeriya, Usman Alkali Baba, da kansa ya jagoranci wani sintirin tabbatar da tsaro a hanyar.
To amma sa'o'i ashirin da hudu bayan wannan sintiri, da 'yan magana ke cewa na fauna tsakuwa don bai wa aya tsoro, sai kawai 'yan bindiga dadi su ka abka wa garin Jere da ke kan hanyar Abuja zuwa kadunan.
'Yan bindigar, sanye da kayan sojoji kuma dauke da manyan bindigogi, sun bi gida gida su na rore mutane kamar wake, hankalinsu kwance, suka Shiga daji da su.
Wani mazaunin garin da abin ya faru a akan idonsa, Bashir Isa Jere, ya shaida wa VOA cewa 'yan bindigar sun shiga garin da misalin karfe Sha daya saura na dare inda suka nufi wani gidan attajirin garin suna tambayar ko nan ne gidan sarki?
Da dai basu gamsu da amsar da aka ba su ba, kai tsaye su ka shiga gidan su ka sankamo shi tare da iyalansa, suka kuma shiga wani gidan ma suka tattara mutanen gidan dama wasu mata da ke diban ruwan famfon tuka tuka duk suka tafi da su.
Mallam Bashir Isa Jere ya ci gaba da bayanin cewa suna kyautata zaton an tsegunta masu wadanda su ka yi niyyar kamawa ne amma kuma su ka yi kuskure.
Duka duka dai sun tafi da mutane goma sha uku daga garin,
Kuma duba da wannan aika aika na zuwa ne sa'o'i 24 da ziyarar shugaban 'yansandan kasar a wannan yanki, Dr Faouk BB Farouk na Jami'ar Abuja na ganin sun yi hakan ne don su nuna sun Isa.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina: