Hedkwatar tsaron Najeriya tace rundunar dakarun operation Hadarin Daji ta sami nasarar hallaka wasu gungun yan bindiga dadi a jihar katsina.
Da yake jawabi a taron manema labaru, daraktan cibiyar tattara bayanai a hedkwatar rundunar tsaron kasar, Manjo Janar Bernard Onyeako yace tun fari dai wani jirgin soji mai leken asiri ya gano inda wasu dandazon yan bindiga suka taru suna gudanar da wani taro a yankin karamar hukumar Dan Musa a jihar katsina.
Take kuma aka tura wasu jiragen yaki inda sukai ruwan wuta tare da karkashe miyagun da ma kwato makamai.
Janaral Onyeako kazalika yace dakarun sun kuma kara kaddamar da wani farmakin na daban inda nanma suka halaka wasu yan bindigar.
Kamar kuma yadda wani mazaunin yankin, Bashir DanMusa ya shaidawa muryar Amurka, lalle kam sun shaida wannan farmaki, inda yace gungun yanbindigar na gudanar da wani bikinsu ne yayinda jirgin yakai harin.
To sai dai kuma duka wannan na zuwane yayinda jihar Kaduna mai makwabtaka da jihar Katsinan ke kara fama da sukurkucewar sha'anin tsaro. Al'amarin dake jan hankalin masana irinsu Dr. Farouk BB Farouk na jami'ar Abuja.
Dr. Farouk ya ce lalle akwai bukatar ace jami'an tsaro ya kassance tsare kasar me biki daya ajandarsu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: