Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karancin Man Fetur: Hukumar DSS A Najeriya Ta Ce Ta Gano Wani Shirin Boye Na Tada Rikici A Yankin Tsakiyar Kasar


Hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Najeriya DSS
Hedikwatar Hukumar Tsaron Farin Kaya Ta Najeriya DSS

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya ta ce ta gano wani shirin boye na tada rikici a wasu yankunan kasar, musamman ma dai yankin arewa ta tsakiyar kasar, inda kuma ake son yin amfani da addini da kabilanci wajen sake wani sabon rikicin ta hanyar ingiza daukar fansa.

Hukumar tsaron ta ce ta gano cewa don cimma wannan manufa, masu daukar nauyin rikicin sun yi taron sirri a ciki da wajen yankunan da ake son haddasa yamutsin, kuma har an nemi 'yan tashi biya da za ai amfani dasu wajen kaddamar da rikicin.

DSS ta ce tana sane da wani shiri da aka kitsa wajen yin amfani da dalibai, da malaman jami'a da a halin yanzu ke yajin aiki da kungiyoyin kwadago, fandararrun matasa da ma wasu muhimman kungiyoyi don kaddamar da wani mummunan yamutsi da zai kai ga bijirewa gwamnati kwatankwacin irin na zanga zangar kin jinin zaluncin yansanda da aka yi a baya na 'ENDSARS.'

Hukumar ta ce ta bankado wani shirin boye na yin amfani da matsalar karancin man fetur ne da ake son yin amfani da shi a matsayin hujjar yin zanga zangar, bayan kuma gwamnati na iya bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar man, a cewar hukumar ta DSS.

Hukumar ta DSS ta ce tana kallon wannan a matsayin rashin kishin kasa kuma tana nan tana bin diddigin duk wadanda ke da hannu wajen yunkurin haddasa wannan tarzoma don cimma wata manufa ta son rai.

Ta kuma gargadi duk masu ruwa da tsaki wajen janyo wannan rikici da su yi wa kansu kiyamullaili, in ba haka ba to ko tabbaci hakika za su yaba wa aya zaki, don doka za ta yi aikinta, inda ta kara tabbatar wa 'yan kasa cewa jami'an tsaro za su ci gaba da kare zaman lafiyar al'umma.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

XS
SM
MD
LG