Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar Hadin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20

Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20.
Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20.

A ci gaba da yakin da take da ‘ƴan kungiyar Boko Haram a Arewa maso gabas, rundunar hadin gwiwa ta MNJTF ta ce tayi nasarar ceto mata shida daga hannun ‘ƴan Boko Haram bayan barin wuta da sojoji a dajin Sambisa.

Wannan na dauke ne cikin sanarwar da mai magana da yawun rundunar Kanal Muhammad Dole ya fitar ranar Alhamis a inda ya ce matan an sace su tsakanin shekarun 2020 da 2021.

Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20
Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20

Matan dai sun fito ne daga jihohin Yobe, Gombe da Adamawa, a inda tuni suna asibiti don duba lafiyarsu tare da ci gaba da bincike kafin a mikasu hannun gwamnati.

Sunayen matan sun haɗa da Grace Daniel ‘yar shekaru 38, Suzan Lazarus ‘yar shekaru 28, Jumai Inuwa shekaru 42, Maria Adamu 27, Martha Malu 27 da kuma Malakalya Dambade 37.

Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20
Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20

Sanarwar ta kara da cewa sojoji sun yi nasarar kashe ‘ƴan Boko Haram da dama a yayin da soja daya ya rasa ransa, wannan nasara ta samu ne biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu a kan wurare irin su Tumbun Fulani, da Tumbun Rago a inda aka kashe ‘yan ta'adda akalla ashirin.

Rundunar ta kara da cewa ta gano wasu gawarwakin ‘yan Boko Haram da dama.

[Alhassan Bala ya bada gudummuwa a rubuta wannan rahoton.]

Saurari rahoto cikin sauti daga Hassan Maina Kaina:

Rundunar Haɗin Gwiwa Ta MNJTF Ta Ceto Mata 6, Ta Kashe ‘Yan Boko Haram 20
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

XS
SM
MD
LG