Yayinda Amurka ta kashe sama da dala miliyan takwas a matsayin gudunmawa a bangaren kiwon lafiya a Najeriya, ta kara jaddada kudirinta na taimakawa wajen gina kasar a matsayin babbar kasa mai kwakkwaran tsarin kiwon lafiya, yaki da cin hanci da tabbatar da gaskiya da adalci
Hedkwatar Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta kwato bindigogi sama da dubu takwas da dari biyu, da kuma sama da harsasai dubu dari biyu daga hannun 'yan ta'adda a baki daya sassa daban daban na kasar.
Hedkwatar Rundunar Tsaron Najeriya ta yi Maraba Lale da cafke jigon kungiyar ‘yan awaren Biafra Simon Ekpa da gwamnatin kasar Finland ta yi.
Babban kwamandan rundunar sojojin Amurka a Afirka Janaral Micheal Langlay ya isa Najeriya inda ya gana da babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron kasar cikin sirri.
Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ne ya fada cikin wata sanarwa da aka fitar cewa Janar Lagbaja dan shekaru 56, ya rasu ne ranar Talata a birnin Legas bayan fama da rashin lafiya
A cewar masanin tsaro, Rabiu Ladodo kamata ya yi a yi wa jami'an tsaro adalci domin ba duk bindigar da ke hanun dan ta'adda ne ta jami'an tsaro ba.
Janaral Buba ya ce abin bakin ciki ne a ce mutanen da a baya suka dau makami suke yakar kasarsu, bayan sun a je makami sun mika wuya, a ce sun kuma sake komawa daji.
Har yanzu ta na kasa ta na dabo game da rikicin 'yan Shi'a da 'yan sandan a Abuja, Najeriya. Hasali ma, 'yan an damke 'yan Shi'a kusan 100 don binciken zakulo masu hannu a kisan 'yan sandan.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce da sanyin safiyar Juma’a Yarima Harry zai gana da Babban Hafsan Hafsoshin rundunar tsaron Najeriya, Janaral Christopher Gwabin Musa.
Wasu daga cikin tsoffin kwamandojin kungiyar Jama'atu Ahlussunnah lil'da'wati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram sun bayyana nadamar irin ta'addancin da suka tafka a matsayinsu na mayakan kungiyar a baya.
Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya shirya wani taro da nufin samar da daidaito tsakanin maza da mata, da kuma yadda za a karfafa mata. Ya kuma duba yadda ‘yan jarida ke ba da rahotannin abubuwan da suka shafi mata.
A ranar goma 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 ne ‘yan ta’addan Boko Haram suka afka makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno, su ka yi awon gaba da kimanin dalibai 276.
Tun dai bayan dawowar daliban Kuriga da na jihar Sakkwato da ‘yan bindiga suka sace domin karbar kudin fansa, ake ta samun ra'ayoyi mabambanta dangane da yadda aka ceto daliban.
Jagoran sojojin Najeriyar ya magantu kan irin kokarin da suke yi na yaki da ta'addanci a cikin kasar, batun binciken harin da soji suka kai kan masu Maulidi a Tudun Biri, kalubalen da sojojin ke fuskanta na karancin makamai da kuma ko gaskiya ne Faransa ta girke sojojinta bataliya biyu a Najeriyar.
Tarayyar Turai EU, ta kudiri aniyar sake daura damara da ganin an sake tsugunar da tubabbun mayakan Boko Haram a kasashen yankin tafkin Chadi domin aiwatar da cikakken zaman lafiya.
Biyo bayan kalubalen tsaro da ya dabaibaye yankin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriyua, rundunar ‘yan sandan birnin ta bullo da wani shirin samar da tsaro mai taken operation VELVET da a cikinsa ake fatan samun sauki.
Domin Kari