ABUJA, NIGERIA —
Shirin Tubali na wanan makon ya bibiyi yadda rashin tsaro ke shafar ayyukan kasuwanci tsakanin kasashen Nijar da makwabciyarta Chadi, ganin yadda ‘yan ta'addan Boko Haram, ‘yan fashi da makami, da wasu miyagu ke cin karensu ba babbaka akan Iyakarsu.
Tuni wannan matsalar ta jefa direbobi da ‘yan kasuwa cikin tashin hankali ganin wannan kalubale na rashin tsaro na ci gaba da kawo cikas.
Saurari cikakken shirin da Hassan Maina Kaina ya gabatar:
Dandalin Mu Tattauna