Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mafi Akasarin Bindigogin Da Ke Hannun ‘Yan ta’adda Na Gwamnati Ne - Ribadu


Mai Baiwa Shugaban Najeriya Shawara Kan Lamarin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu
Mai Baiwa Shugaban Najeriya Shawara Kan Lamarin Tsaro, Malam Nuhu Ribadu

A cewar masanin tsaro, Rabiu Ladodo kamata ya yi a yi wa jami'an tsaro adalci domin ba duk bindigar da ke hanun dan ta'adda ne ta jami'an tsaro ba.

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya zargi wasu ‘yan sanda da sojoji da sayarwa da ‘yan ta'adda makamai ko ba su haya, irin makaman kuma da ake amfani da su wajen hallaka jami'an
tsaron.

Mallam Nuhu Ribadu wanda ke jawabi yayin gangamin lalata bindigogi kimanin 2,400 da hukumar hana yaduwar makamai ta Najeriya ta yi a wajen birnin Abuja, ya ce duk jami'in tsaron da zai sayar wa da ‘yan ta'adda makami to tabbas wannan ya wuce kidnapa ko dan Boko Haram

Lokacin da ake kona makamai
Lokacin da ake kona makamai


Dama dai an dade ana zargin wasu baragurbin jami'an tsaro na sai dawa ‘yan ta'adda makamai, zargin da hukumance mashawarcin shugaban kasa kan tsaron ya tabbatasr da shi, yana mai cewa:

''Eh, yana faruwa, tabbas yana faruwa, bindigogi masu yawan gaske da ke hanun 'yan ta'adda ainihinsu na gwamnati ne, haka siddan a dauka a sayar da ko ba da su haya, wannan wane irin masifa ce? dole a dakatar da hakan, dole mu yaki ire-iren wadannan shaidanun jami'ai.''

Mallam Nuhu Ribadu ya ce akwai kuma wasu mutane can wata nahiya suna kekkera makamai suna kawo mana wannan nahiyya don mu karkashe junanmu.

Ya kuma buga misali da abin da ke faruwa a yankin Sahel wanda ya ce na fama da matsalar da ba wani yanki a duniya da ke fama kamarsa, inda mutane ke cikin yunwa, amma sai ake kawo masu makamai suna hallaka junansu, maimakon a kawo masu ci gaban kimiyya don inganta rayuwarsu.

Taron kona makamai a wajen birnin Abuja
Taron kona makamai a wajen birnin Abuja

Tunda farko sai da shugaban hukumar hana yaduwar kananan makamai ta Najeriya DIG Babatunde Kokuma ya yi bayanin cewa an samo makaman ne daga hanun ‘yan ta'adda ta hanyar soji da ‘yansanda da sauran jami'an tsaro, da ma wanda ‘yan ta'addan da suka yi saranda suka mikawa hukuma, sannan nan gaba kadan za a lalata makaman da hukumar kwastam ta cafke

A cewar masanin tsaro Kwamishinan ‘yansanda Rabiu Ladodo kamata ya yi a yi wa jami'an tsaro adalci domin ba duk bindigar da ke hanun dan ta'adda ne ta jami'an tsaro ba.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina daga Abuja:

Mafi Akasarin Bindigogin Da Ke Hannun ‘Yan ta’adda Na Gwamnati Ne - Ribadu.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:09 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG