Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kwararowar 'Yan Bindiga Daga Yankin Sahel, Na Haddasa Karuwar Ayyukan Ta'addanci A Najeriya...


Major General Easa Buba
Major General Easa Buba

Hedikwatar rundunar tsaron Najeriya ta ce tuttudowar 'yan ta'adda daga yankin Sahel ya dada haifar da karuwar hare haren ta'addanci a Najeriya.

A wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar rundunar tsaron kasa da ke Abuja, daraktan sashen tattara bayanai kan fafatawa da sojojin Najeriya su ke yi, Manjo Janar Edward Buba, ya ce a 'yan kwanakin bayan nan, ana samun karuwar hare haren ta'addanci.


Manjo Janar Buba, ya ce 'yan bindigar su na kwararowa ta wurare irin su Kareto, Wajiroko, Chibok, Gwoza da sabon gari a jihar Barno, sai Gudu, Illela, Sabon Birni da sauran wurare a yankin arewa maso yammacin Najeriya. Daraktan ya ce ana samun ta'azarar hare haren ne saboda yadda mayakan na ketare suke samun goyon bayan abokan aika aikarsu wadanda suke tsegunta masu kai komon sojoji.

Ya ce ko da yake sojoji suna fuskantar dan koma baya a wasu bangarori, suna samun kwarin gwiwar karya lagon abokan gaba.

Da yake tsokaci akan wannan batu, shugaban kamfanin tsaro na BEACON INTEL Dr. Kabiru Adamu, ya ce bisa yadda bincikensu ya nuna, akwai alamun bakin 'yan ta'adda na tuttudowa cikin Najeriya kuma abin da ya haddasa hakan shi ne tsamin dangantaka da ke tsakanin Najeriya da makwabciyar ta Nijar da kuma fatattakar 'yan ta'adda da kasar Tchadi ta yi daga kasarta.

A latsa nan domin sauraron rahoton Hassan Maina kaina:

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG