Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ofishin Jakadancin Amurka A Najeriya Ya Shirya Wani Taron Karfafa Harkokin Mata


Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya shirya wani taro da nufin samar da daidaito tsakanin maza da mata, da kuma yadda za a karfafa mata. Ya kuma duba yadda ‘yan jarida ke ba da rahotannin abubuwan da suka shafi mata.

Mukaddashin babban jami’in diflomasiyyar Amurka a Najeriya, Mr. Brown, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana yadda ‘yan jarida a Najeriya ke nuna gazawar mata, wani lokaci ma da cin fuska a yayin ba da rahoton abin da ya shafi mata da ke siyasa ko kuma wadanda ke rike da mukaman gwamnati.

Mr. Brown ya ce baki daya kasa da kashi shida cikin dari ne adadin mata da ke rike da mukaman siyasa a hukumomin gwamnati a Najeriya. Ya kuma ambaci wani rahoto da wata cibiyar bincike a kan ci gaban kasa ta fidda, wanda ya bayyana yadda ake yi wa mata wani gani gani.

Hassan Aliyu Karofi, jami’i ne a cibiyar da ta gudanar da binciken, ya shaida wa Muryar Amurka cewa rahoton da suka kwashe watanni tara suna bincike a kai ya nuna yadda mata 'yan siyasa ko wadanda ke rike da mukaman gwamnati ke fuskantar kalubale iri-iri, kawai don kasancewarsu mata.

Rahoton ya kuma nuna yadda al’ada ke takaa rawa wajen nuna rashin dacewar mata su yi shugabanci, wadanda ma suka sami sa’ar samun mukamin yawancin lokuta sai a yi masu wani kallo na kaskanci.

Karofi ya ce rahoton ya cewa kalubalen da mata a kudanci da arewacin Najeriya ke fuskanta kusan daya ne, inda al’ada ke da matukar tasiri. Sai dai a kudancin kasar al’amarin da sauki.

Ita ma tsohuwar shugabar kungiyar ‘yan jarida mata ta Najeriya (NAWOJ) Ladi Bala, ta shaida wa Muryar Amurka cewa mata na fuskantar kalubalen nuna wariya da kyara a wuraren aikinsu da ma idan suka je yin aikin.

Ta na mai cewa sau tari kafafen sadarwa ba kowane aikin dauko rahotanni ake sa mata ba, ana ganin kamar wasu fannonin na maza ne kadai, mace bata cancanci aiki a nan ba. Al’amarin da ta ce wannan ba daidai bane.

Da yake maida martani, shugaban kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, NUJ, Mr. Chris Isunazo, ya ce suna gudanar da shirye shirye don wayar da kan ‘yan jarida da ma jagororin kafafen sadarwa don cike wannan gibi.

Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:

Ofishin Jakadancin Amurka A Najeriya Ya Shirya Wani Taron Karfafa Harkokin Mata .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG