Tun da jimawa masana da masu sharhi kan al'amuran tsaro suke dora ayar tambaya akan inda 'yan Boko Haram suke samun kudaden da suka shafe sama da shekaru 15 suna cin karen su ba babbaka a yakin da yaki ci yaki cinyewa.
Wakilin Muryar Amurka Hassan Maina Kaina, ya ruwaito cewa, a bayanin da babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriya Janar Christopher Musa yayi masa, ya ce “Akwai wadanda suke taimaka musu ('yan Boko Haram), shi ya sa suke iya sayen makamai duk tsadar sa. Sannan kan iyakokin mu basu da wadatacen tsaro".
Da Hassan Maina Kaina ya tuntubi masanin tsaro a jami’ar Maiduguri, Dr. Muhammad El-Nur Dongel, ya gaskata bayanan Janar Christopher Musa sannan ya kara da cewa "babu yadda za Janar Musa zai yi magana mara tushe ko ma’ana".
"Batun cewa kungiyar tana samun tallafin kudade daga kasashen waje, gaskiya ce kuma suna da buri domin babu yadda za ayi wani bako ya shiga gari ba tare da samun wani alkhairi ba kuma duk sun na da nasaba da tattalin arziki. Akwai ma’adanai kuma masu daukan nauyin ta’addanci, sun san cewa mun sani".
Sai dai mahangar masanin tsaro wanda yayi aiki a matakin kasa da kasa, kwamanda Musa Isah Salmanu mai ritaya ya dan banbanta.
Ya ce "ba wai gwamnatin kasashe ne ke tallafa musu da kudade ko kuma halastatun kungiyoyi ne ke bada kudaden ba. Akwai masu aikata laifuka da kuma laifuka da ake aikatawa akan iyakokin kasashe wanda ke baiwa 'yan Boko Haram damar samun kudaden wasu kasashe".
A latsa nan, domin sauraron rahoton Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna