Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarihin Marigayi Babban Hafsan Hafsoshin Rundunar Sojojin Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja


Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja
Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja

Mai magana da yawun fadar shugaban kasa Bayo Onanuga ne ya fada cikin wata sanarwa da aka fitar cewa Janar Lagbaja dan shekaru 56, ya rasu ne ranar Talata a birnin Legas bayan fama da rashin lafiya

Fadar shugaban kasar Najeriya ce ta sanar da rasuwar Babban Hafsan Hafsoshin rundunar sojojin kasar, Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja.

A wani mataki na karrama marigayin shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya soke taron majalisar zartaswa da za a yi yau Laraba.

Shugaba Tinubu kazalika ya kuma bada umarnin a saukar da tutar kasar a ko'ina cikin kasar na tsawon kwanaki bakwai inda ya mikawa iyalai da rundunar sojin kasar ta'aziyar wannan babban rashi.

Babban hafsan hafsoshin rundunar tsaron Najeriya, Janar Taoreed CG Musa wanda ya nuna alhininsa bisa wannan rashi, ya bayyana rashin a matsayin wani babban al'amari ga kasa.

Janar CG Musa ya bayyana Janar Lagbaja a matsayin wani jajirtaccen soja, mai aiki tukuru, amintacce abin amincewa mai aiki bisa gaskiya da jajircewa, yana mai cewa ba karamin gibi wannan rashi ya haifar ba.

Babban hafsan rundunar tsaron ya kara da cewa irin kwazon aiki na Lgbaja a gidan soja da hangen nesansa yasa shi samar da sashin sojin sama a rundunar sojin kasa, da kuma irin rawar da ya taka a fagen daga a cewar Janar CG Musamusamman a rundunonin Operation Forest Sanity , a jihar Kaduna da Niger, da kuma Operation Lafiya, Operation Hadin Kai Dole, OOperatio zaman lafiya a jihar Borno, Operation Zaki a jihar Benue da Operation Udo Kaa a
jihohin kudu maso gabas ya taimaka wajen saisaita al'amura a
fannin tsaron kasa.

A can mahaifarsa kuma, gwamnan jiharsa ta OSUN Ademola Adeleke ya bayyana rashin a matsayin wani babban gibi maras dadi da ya afkawa jihar da ma iyalan babbar zuriyar Lagbaja, inda ya kara da cewa ''Mun yi rashin dan'uwa mai hangen nesa tare da jagorantar rundunar soji cikin kwarewa da gudanar da sauye-sauyen da ke tafiya da zamani, wanda cikin dan kankanin lokaci da ya yi yana jagorantar rundunar ya samar da wani irin kyakkyawan yanayin fatattakar ‘yan ta'adda da ‘yan bindiga''

Gwamna Adeleke ya ce cikin haduwarsa ta karshe da marigayin, ya bayyana masa cewa yana da kyakkyawar fatan samun amintacciyar kasa Najeriya da sojojin dake zama kan gaba a matsayin alamar hadin kan kasa.

Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja akan babur, za su je yakar ‘yan bindiga
Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja akan babur, za su je yakar ‘yan bindiga


TARIHIN MARIGAYI JANAR LAGBAJA
An haifi Janar Lagbaja ranar ashirin da uku ga watan Fabrairin shekarar alif dari tara da sittin da takwas a kauyen Ipopu dake yankin Irepodun na jihar Osun, ko da yake, ya yi wani adadi mai yawa na farkon rayuwarsa a garin Osogbo inda ya halarci makaranta Saint Chales Grammer School, daga nan kuma ya garzaya kwalejin horon malamai.

Marigayi Lagbaja ya samu gurbin karatu a makarantar horas da hafsoshin soji wato NDA da ke Kaduna a shekarar 1987, dan kwas 36, wanda ya kammala a shekarar 1992.

Janar Lagbaja wanda ya shafe fiye da shekaru talatin yana aikin soja, ya rike mukamai daban-daban a gidan soja kafin nada shi matsayin babban hafsan hafsoshi.

Wani babban abin da za a tuna da marigayi Lagbaja shine yadda shi da kansa a matsayinsa na babban kwamanda wato GOC a runduna ta daya dake Kaduna inda shi da kansa yake jagorantar fafatawa da ‘yan bindiga.

A wannan runduna ne dai Janar Lagbaja ya sauya salon yakar ‘yan ta'addan inda shima ya bullo da sojoji masu yaki akan babura, kamar dai yadda suma ‘yan ta'addan ke yi, kuma sau da dama shima ya kan fita yakin akan babur a fafata dashi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG