Da suke tattaunawa da sashen Hausa na Muryar Amurka, daya daga cikin hadiman dake zama daya daga cikin hadiman tsohon shugaban kungiyar Abubakar Shekau, kuma daya daga cikin wadanda suka sace daliban Chibok, ya ce abin da suka yi a baya hakika bai dace ba, kuma babban abin takaici ne.
Ya ce ya san Abubakar Shekau shekaru da dama kafin ma a fara rikicin na arewa maso gabas, ko da aka ji wa shekau din rauni, an kawoshi Damaturu, inda yake jinya kuma a lokacin shike yi masa 'yan aikace-aikace da wanki da da sauransu.
Bayan da kuma Shekau ya koma daji sukan aika masa da kudi don biyan bukatun yau da kullum kafin daga bisani shima ya bisu dajin, inda bayan samun horo, shima ya zama cikakken kwamandan dake jagorantar kai hare hare.
Wannan tsohon kwamandan da ya ce ya jagoranci kai hare hare a sassan arewa maso gabas da dama, yayi ikirarin kashe fararen hula da sojojin da bai san adadinsu ba, al'amarin kuma da ya ce yana matukar bakin cikin hakan.
Bugu da kari, ya kuma yi bayanin yadda ya taka rawa yayin sace daliban Chibok inda suka kaisu dajin Sambisa, koda yake ya ce shi bai auri ko daya ba, amma abokansa da dama sun auresu.
Ya ce babban abin da ya sa ya fice daga kungiyar ta'addancin shine yadda ake sa su karkashe mutane wasu ma ta hanyar yankan rago ba gaira ba dalili.
Da kuma yake amsa tambayar ko ina Leah Sheribu take? daliba daya tilo daga cikin daliban Dapchi da ta rage a hanun yan ta'addan, wannan tubabben kwamandan na Boko Haram ya ce LEAH tana hanun mayakan Boko Haram tsagin ISWAP a yankin tafkin Tchadi.
Ya ce abokansu ne ke rike da ita, kuma sun mata aure har ta haifi yara biyu, namiji da mace, koda yake mijinta na farko ya rasu, amma wani dan ta'addan ya sake aureta.
Domin karin bayani saurari rahotan Hassan Maina Kaina.
Dandalin Mu Tattauna