Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills ya ce kasarsa ta kashe kimanin dala miliyan takwas da dubu dari uku wajen samar da magungunan rage radadin cuta mai karya garkuwar jiki a Najeriya
Jakadan ya ce Amurkan za ta ci gaba da tallafawa a fannonin kiwon lafiya, tabbatar da gaskiya da yaki da cin hanci.
Ya bayyana rashin gaskiya ko cin hanci a matsayin babban abin da ke kawo cikas ne ga bangaren kiwon lafiya a kasar.
Ya ce idan aka karkatar da kudaden da yakamata a sayo magunguna, ko odar jabun magunguna ko kuma gaza biyan jami’an kiwon lafiya hakkokinsu wannan duk ka iya sanadiyyar salwantar rayukan jama’a, a kasar.
Da yake tsokaci kan al’amarin, Farfesa Ibrahim Maqari ya nuna takaici ganin yadda cin hanci ya zama ruwan dare a Najeriya ta yadda wasu ke ganin rayuwa ba za ta yiwu ba, batare da cin hanci ba.
Inda ya nuna lalle kuwa idan ana son samun gyara to ya zama dole sai an yi karatun ta natsu.
Shima wani kwararren likita Dr. Sale Abba ya nuna irin alakar da akwai, tsakanin kyakkyawan shugabanci da ingatacen tsari irin na kiwon lafiya.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna