Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cika Shekara 10 Da Sace Daliban Makarantar Chibok


Daliban Makarantar Chibok
Daliban Makarantar Chibok

A ranar goma 14 ga watan Afirilun shekarar 2014 ne ‘yan ta’addan Boko Haram suka afka makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Chibok a jihar Borno, su ka yi awon gaba da kimanin dalibai 276.

An iya ceto dalibai 128 tun daga lokacin zuwa yanzu, amma har yanzu sauran dalibai 91 da suka rage, ba a san halin da suke ciki ba kuma ba amo ba labarinsu.
Ranar Lahadi 14 ga watan Afirilu aka cika shekaru goma da sace daliban, gwamnatin Amurka ta aike wa gwamnatin Najeriya sakon karfafa gwiwa da ya bayyana cewa Amurka na tare da Najeriya a irin wannan lokaci na juyayi.

A wata sanarwar da ofishin jakadancin Amurka a Abuja ya aike wa sashin Hausa na VOA, Amurka ta ce tana goyon bayan daliban na Chibok da suka tsira daga wannan bala’in, da iyalansu, da kuma duk sauran wadanda suka fuskanci ta’asar ‘yan ta’adda a baki dayan kasar.

Daya daga cikin jagororin al’ummar Kibaku, kuma shugaban kungiyar iyayen daliban na makarantar Chibok, Mr. Ayuba Alamson, da sassanyar murya ya shaida wa Muryar Amurka cewa a cikin shekaru goman nan suna rayuwa cikin takaici da kunci saboda rashin sauran daliban da ke hannun mayakan.

Satar daliban makarantar Chibok ya haifar da kafa kungiyar fafutikar ceto daliban mai suna “Bring Back Our Girls,” kuma daya daga cikin kashin bayan kungiyar Dr. Emman Shehu ya bayyana cewa suna cikin takaici, saboda yau shekaru goma kenan amma an kasa gano inda sauran ‘yan matan suke, ya na mai cewa wannan abin damuwa ne sosai.

Masu Zanga-Zanga sun bukaci Gwamnati dasu kubuto da 'yan matan Chibok da aka sace, 14 ga Oktoba 2014.
Masu Zanga-Zanga sun bukaci Gwamnati dasu kubuto da 'yan matan Chibok da aka sace, 14 ga Oktoba 2014.

Dr. Shehu ya kara da cewa lamarin ya nuna akwai sauran jan aiki a gaban gwamnati da jami’an tsaro, kuma akwai bukatar jan damara wajen kare hakkokin jama’a, musamman marasa galihu a cikin al’umma.

Dr. Shehu ya ce a lokacin da aka sace daliban, shugaba Tinubu shi ma ya nuna goyon baya ga fafutikar ‘yan kungiyar Bring Back Our Girls, har ma ya daga allon da ke nuna bukatar maido da daliban. Don haka yanzu ne ya kamata yayi amfani da ikon kujerarsa wajen ceto sauran daliban, a cewarsa.

To ko akwai yiwuwar iya kubutar da sauran daliban, duba da tsawon shekarun da aka shafe suna hannun ‘yan ta’adda? Masanin tsaro Wing Commander Musa Isa Salman, ya ce ba za a cire tsammani ba, ganin cewa a baya wasu da suka shafe shekaru a cikin daji a hannun ‘yan ta’addan sun iya dawowa, ko kuma an cetosu.

Kwamanda Salman ya kara da cewa gwamnati zata iya amfani da kungiyoyin agaji irin su Red Cross ko kuma tubabbun ‘yan ta’addan wajen ceto sauran ‘yan matan.

Saurari rahoton cikin sauti:

An Cika Shekara 10 Da Sace Daliban Makarantar Chibok
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:45 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG