Injiniya Faruk Ahmed ya bayyana hakan ne a Wata Hira ta musamman da Muryar Amurka, inda ya yi kira ga 'yan Najeriya da su shiga farga tare da mika bukatar dilallan man fetur su buda gidajen mai, su rika sayar da man saboda kamfanin NNPCL ya tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da zai ishi 'yan kasa
Kamfanin kasuwancin man fetur na Najeriya wato NNPCL ya tabbatar da cewa akwai wadataccen mai da zai ishi 'yan kasa na kimanin kwanaki 30 duk da cewa an fara ganin dogayen layukan mai tun da maraicen ranar Litinin,.
Sabon shugaban Najeriya da ya harbi rantsuwar kama aiki a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Bola Ahemd Tinubu, ya sha alwashin yin gagarumin garambawul da ta da komadar tattalin arzikin kasar ta hanyoyi daban-daban.
Kotun koli a Najeriya ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP ta shigar ta na kalubalantar tsayawar Sanata Kashim Shettima takara a mukaman siyasa biyu, wato amincewa da zama mataimakin shugaban kasa da kuma sayen tikitin neman kujerar Sanata a majalisar dattawan Najeriya.
Jim kadan bayan ci gaba da zaman sauraron kararrakin Zaben shugaban kasa na watan Fabrairu, a yau Litinin kotun ta yi watsi da bukatar da jam’iyyun Leba da PDP suka shigar ta neman a rika yada duk zaman kotun da za a yi kai tsaye a kafafen yada labarai.
A kwana ta hudu da fara zama, kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta dage zamanta na sharar fagge a karar da jam’iyyar PDP da dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar suka shigar gabanta zuwa ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, 2023.
A zaman da ta yi ranar Laraba 10 ga watan Mayu, kotun sauraron kararrakin kalubalantar nasarar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben 2023 ta yi watsi da karar da jam’iyyar APP ta shigar bayan da lauyan da ke kareta ya ce sun janye karar.
Kasa da sa’o’i 48 da fara zaman share fagen sauraren shari’a a karar da jam’iyyun daban-daban suka shigar kan sakamakon zaben shekarar 2023, kotun ta dage zaman shari’ar da PDP ta shigar da hukumar INEC, APC, da Bola Tinubu zuwa ranar Alhamis 11 ga watan Mayu.
Kotun musamman ta sauraren kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya da ke zama a Abuja ta fara shara Faggen zaman sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da aka shigar a gabanta.
Kungiyoyin raya kasa sun yi taro domin tabbbatar da zaman lafiya a Najeriya, tabbatar da zaman lafiya da hadin kan 'yan Najeriya bisa la'akari da irin kalaman da wasu 'yan siyasa da basu ji dadin yadda sakamakon zabe ya kasance ba.
Babban bankin Najeriya ya ce yana ci gaba da buga sababbin takarkun kudi, sai dai har yanzu 'yan Najeriya na kokowa da cewa, suna cigaba da fuskantar matala wajen samun takadun kudin.
Karamin ministan albarkatun man fetur na Najeriya Timipre Sylva ya yi murabus daga mukaminsa a kasar domin neman sabon wa'adi a matsayin gwamnan jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a yankin Neja Delta.
A wani mataki na kara yawan man da ke rumbunta na ajiya daga biliyan 37 zuwa 50 da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa, gwamnatin Najeriya ta kaddamar da aikin tono mai a matakin farko a yankin Ajibu wato Kayarda da ke karamar hukumar Obi na jihar Nasarawa.
A wani mataki na kara yawan man dake rumbunta na ajiya daga biliyan 37 zuwa 50 da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar gwamnatin Najeriya ta kaddamar da aikin tonon mai a matakin farko a yankin Ajibu wato Kayarda dake karamar hukumar Obi na jihar Nasarawa.
A yayin da bankunan kasuwanci suka bude kofofinsu don hada-hadar kudi a Najeriya a ranar Asabar da Lahadi bisa umurnin babban bankin kasar domin samun saukin matsalar karancin takardun kudin Naira, wasu masu kanana da matsakaitan sana’o'i sun ce matakin na CBN ya fara tasiri.
Domin Kari