Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar PDP Da Leba Na Neman Ta Rika Nuna Zamanta Kai Tsaye A Kafafen Yada Labarai


Kotu
Kotu

Jim kadan bayan ci gaba da zaman sauraron kararrakin Zaben shugaban kasa na watan Fabrairu, a yau Litinin kotun ta yi watsi da bukatar da jam’iyyun Leba da PDP suka shigar ta neman a rika yada duk zaman kotun da za a yi kai tsaye a kafafen yada labarai.

Ta yi hakan ne don gamsar da yan kasa da ke ciki da wajen Najeriya cewa ana sauraron zaman kotun a bayyane ba tare boye wani abu ba.

Kotun ta bayyana matsayar ta a game da bukatar Jam’iyyun Leba da PDPn na neman a rika yada zaman shari’ar ta kai tsaye kullum a kafaffen yada labarai ne bayan yin nazari a kan jawaban dukkan lauyoyin bangarorin da shari’ar ta shafa tsakanin tawagar lauyoyin kotun 5 da ke samun jagorancin mai shari’a Haruna Simon Tsammani sannan ta yanke hukuncin yin watsi da bukatar, ta na mai cewa kin amincewa da bukatar yada shari’ar a gidan talabijin kai tsaye ba ya nufin cewa kotun ba za ta yi wa kowa a bangaren karar da aka shigar adalci ba.

Zaman kotu a Jos
Zaman kotu a Jos

Da ya ke gabatar da matsayar kotun na yau Litinin, jagoran tawagar lauyoyin kotun sauraron kararrakin zaben mai shari’a Haruna Tsamani ya bayyana cewa bukatar da mai shigar da kara ya nema ya fita daga cikin hurumin kotu a kararrakin da aka shigar kuma ya sabawa doka tun da babu inda doka ta fayyace za a iya yada zaman shari’a kai tsaye wa duniya a lokacin da ake tsaka da zaman kotu yana mai cewa kundin tsarin mulki ne ya kafa kotun kuma tana aiki ne a karkashin dokar kotun daukaka kara ta Najeriya.

Sai dai kakakin jam’iyyar Leba, Dakta Yunusa Tanko ya bayyana rashin jin dadinsu a game da hukuncin kotun na yin watsi da bukatar jam’iyyarsa ta Leba da ta nemi kotu ta bada damar a rika yadda zaman shari’ar karar da ta shigar kai tsaye yana mai cewa sun nemi hakan ne don yan Najeriya su rika ganin yadda shari’ar ke wakana kai tsaye ba sai an basu labari ba.

A nasa bangare, sakataren yada labaran jam’iyyar PDP a matakin kasa, Debo Ologunagba, ya bayyana cewa tabas ba su ji dadin hukuncin da kotu ta zartars na yin watsi da bukatar jam’iyyarsa ta PDP da dan takararta, Atiku Abubakar na neman a rika nuna zaman kotun kai traye a kafoffin yada labarai ba, amma suna da yakinin cewa kotu zata yi musu adalci ganin irin shaidu da hojojjin da suke da su da zasu tabbatar da cewa an yi magudi a zaben na watan Febrairu kuma sun yi imanin cewa kotu zata yi adalci ta baiwa ‘yan Najeriya wanda suka zaba.

Barrister Mainasara Kogo ya ce hukuncin kotun ya yi daidai duk da cewa babu inda dokar kasar ta fayyace cewa a yi zaman koto a banyans ko a cikin sirri.

Kazalila, a yayin bayyana matsayar na kotu kuma, mai shari’a Tsammani ya ce an kafa kotun ne a bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya domin ta saurari kararraki da ke gabanta a game da zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 25 ga watan Febrairun kuma ba za ta iya zama mai karo abunda baya bisa tamarin dokar kasa ba inda ya kara da cewa ya kamata a gujewa wani abunda zai matsawa kotu ta yadda ba zata yi kuskure a aikinta ba.

A yayin zaman na yau dai kotun tantance shaidu da jam’iyyar Allied Peoples Movement wato APM ta gabatar a daidai lokacin da ake ci gaba da kalubalantar nasarar zababben shugaban kasa Bola Tinubu a zaben da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Saurari rahoton Halima Abdulra'uf:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG