Shugaban hukumar NMDPRA mai kula da dokokin fannin albarkatun man fetur da iskar gas ta Najeriya, Injiniya Faruk Ahmed ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da dillalan man fetur a birnin tarayya Abuja, inda ya jaddada bukatar masu ruwa da tsaki su bi kai’dodin neman lasisi don shigowa da mai kamar yadda doka ta tanadar, ya kuma ja kunnen dillalan da su guji cutar da 'yan kasa ta hanyar sanya farashi fiye da yadda ya kamata.
Malam Yabagi Sani, masani ne a fannin albarkatun man fetur a Najeriya, ya bayyana cewa matakin da hukumar NMDPRA ta dauka ya zo daidai da akidar tafiya da tattalin arzikin kasa wanda ya dogara ga tsarin kasuwanci na kasa, wanda gwamnati ba ta shiga harkokin kasuwanci, da sauransu, sai da ta nemo hanyoyin tallafa wa 'yan kasa.
A nasa bangaren mataimakin shugaban kungiyar dillalan man fetur masu zaman kansu ta Najeriya wato IPMAN, Abubakar Maigandi Dakingari, cewa ya yi muddin aka cika alkawarin bada lasisi kamar yadda aka fada, to su ma dillalan man fetur masu zaman kansu zasu iya shigo da man, amma damuwarsu ita ce har yanzu kamfanin kasuwancin man fetur na NNPCL ya rike musu kudi ba tare da basu kaya ba tsawon watanni 8.
Sai dai nan take kamfanin NNPCL bai ce komai ba game da batun na kungiyar IPMAN.
A yayin da ‘yan Najeriya ke fatan ganin an samu daidaito a farashin kowacce litar man fetur wanda ya karu da sama da kaso 156 cikin 100, wato daga Naira 195 zuwa sama da Naira 500 kan kowacce lita a kusan duk jihohin kasar da kuma babban birnin tarayya, shugaba Tinubu ya roki 'yan kasar da su kara hakuri don nan bada jimawa ba gwamnatinsa zata samo wasu hanyoyin kawo sauki musamman a bangarorin sufuri, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi ga 'yan kasar, da dai sauransu.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: