Yin watsi da karar da jam’iyyar Action People’s Party (APP) da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi a karkashin jagorancin mai shari’a Haruna Simon Tsammani na zuwa ne biyo bayan mika bukatar hakan da lauyan jam’iyyar APP ya yi a gaban kotu, kuma wannan shi ne karo na biyu da aka yi hakan tun bayan fara sauraron kararrakin kalubalantar ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban Najeriya da zai gaji shugaba Muhammadu Buhari wanda ke karasa wa’adin mulkinsa karo na biyu a karshen watan Mayu.
A yayin zaman kotun na ranar Laraba 10 ga watan Mayu, bayan sauraron jam’iyyar da ta shigar da kara da tawagar lauyoyin da ke kare hukumar INEC, jam’iyyar APC da dan takararta Bola Ahmed Tinubu, lauyan jam’iyyar APP, barista Obed O. Agbo, ya bayyana matsayin jam’iyyar da yake karewa na janye karar da ta shigar a gaban kotu, daga bisani kotu ta yi watsi da kara.
Barista Agbo ya ce ya janye karar ne bisa umarnin jam’iyyar da yake karewa, yana mai cewa shi a shirye yake ya yi aikinsa amma dole ne ya bi umarnin wadanda suka bashi aiki.
Daya daga cikin lauyoyin dake kare zababben shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a gaban kotun sauraron kararrakin zaben Dakta Hassan, mai mukamin SAN, yace da maraicen ranar Talata ne lauyan da ke kare jam’iyyar APP ya sanar da niyyar janye karar wadanda yake karewa kuma ya gabatar da matakin a gaban kotu, abinda ya sa alkalin kotun ya yi watsi da karar ta jam’iyyar APP.
Matakin kotun na nufin saura kararrakin uku a gabanta a yanzu daga guda biyar da aka shigar, bayan janye kararraki biyu da jam’iyyun AA da APP suka yi.
Daya daga cikin lauyoyin da ke kare Tinubu a kotu, barista Gani Rotimi Arodo, ya ce matakin da jam’iyyun suka dauka ya kawo sauki a aikin ci gaba da sauraron kararrakin. Ya kara da cewa ta yiwu gamsassun bayanai da suka yi wa jam’iyyar APP ko kuma kishin kasa ne suka sa ta janye karar a gaban kotu.
Kotun dai ta dage sauraron karar da jam’iyyar Labour ta shigar zuwa ranar 17 ga watan Mayu bayan bukatar da lauyoyin bangarorin da ake kara suka mika a kan a basu karin lokaci don duba batun cancantar bukatar nuna zaman kotu kai tsaye a kafafen yada labarai.
A gefe guda kuma, an yi taho mu-gama tsakanin masu zanga-zangar mara wa kotu baya a kan ta ci gaba da sauke nauyin da dokar kasa ta dora mata da wani mutum mai dauke da tutocin Najeriya biyu wanda ke adawa da ayyana Tinubu a matsayın zababben shugaban Najeriya, da ke cewa ba za a saida kasarsa ga ‘yan jari hujja ba.
Saurari rahoton Halima Abdulrauf: