Matakin na babban bankin Najeriya (CBN) na zuwa ne kwanaki 17 bayan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dare kan karagar mulki, ya kuma yi daidai da alkawarin da shugaban ya dauka na hada kan farashin canjin kudade dabam-dabam, ciki har da na bankunan kasuwanci da na 'yan canjin bayan fage.
A cikin shekaru da yawa da suka gabata, masana harkar tattalin arziki da cibiyoyin kula da hada-hadar kudi na duniya sun nuna damuwa game da tsarin canjin kudi na kasar, musamman yadda yake shafar mutane a ciki da wajen kasar ta fannin kasuwanci.
Masanin tattalin arziki kuma malami mai koyarwa a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Muhammad Muttaka Usman, ya ce matakin CBN zai bai wa bankunan kasuwanci damar su rinka neman kudaden waje da kansu sannan su nemi yadda zasu sayar, kuma hakan na nufin cewa farashin kudaden wajen su yi sama amma daga bisani za a sami daidaito.
Alhaji Umar Mairiga, tsohon ma’aikacin babban bankin CBN ne, ya bayyana cewa matakin CBN abu ne da 'yan kasuwar ciki da wajen kasar ke dako kuma ba zai yi mummunan tasiri ga farashin kayayyaki a kasar ba.
A nasa bangaren, shugaban kungiyar 'yan kasuwannin canjin bayan fage a matakin kasa Alh. Aminu Gwadabe, ya yi marhaba da matakin babban bankin tare da yin shimfida a kan yadda kasuwancin canjin kudi na bayan fage ya samo asali a Najeriya.
A lokacin da ya gabatar da jawabin farko bayan ya sha rantsuwar kama aiki, shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta daidaita tsarin musayar kudaden waje a kasar, a matsayin wani bangare na babban shirin kawo sauyi a fannin tattalin arziki mafi girma a nahiyar Afirka.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: