Kotun ta ce ta yi haka ne don baiwa dukkan wadanda al’amarin shari’ar ya shafa su warware matsalolin da suka taso a zaman ta na ranar Talata saboda a iya fara ainihin zaman shari’ar a kan lokaci.
Mai shari’a Haruna Simon Tsammani dake jagorantar tawagar manyan alkalai 5 da suka hada da Mai shari’a Misturat Bolaji-Yusuf, Stephen Adah, Boloukuoromo Moses Ugo, Abba-Bello Mohammed ne suka dage zaman sauraron sharr fagen don baiwa bangarorin da shari’ar ta shafa damar warware ababen da suka taso, kama daga mika wasu bukatu da kuma takardun da ya kamata a shigar a gaban kotun daga yau zuwa ranar Alhamis 11 ga watan Mayun nan.
Shugaban jam’iyyar PDP na rikon kwarya, Ambasada Umar Aliyu Damagum, da ya wakilci jam’iyyarsa a yayin zaman kotun, ya ce duk da cewa suna sane da yunkurin da wadanda aka kai kara suke yi na bata lokaci kan shari'ar, sun yi imanın cewa za’a yi abinda ya kamata ganin yadda alkalin kotun ya sha alwashin tabbbatar da cewa za'a zartar da shari’ar yadda ya kamata.
Damagum ya kuma ce idan kotu ta amsa bukatarsu ta neman a bari a yada zaman sauraron karar tasu kai tsaye wa 'yan Najeriya da ma duniya baki daya, hakan zai kara karfafa musu gwiwa a shari’ar.
A wani bangare kuma daya daga cikin tawagar lauyoyin da ke kare jam’iyyar PDP da dan takararta, Atiku Abubakar a kotu, Daniel Bwala, ya bayyana cewa adadin kwanaki 180 ne doka ta bayar a fara tare da gama shari’ar kararrakin bayan zabe.
Ya ce har yanzu suna da kwarin gwiwar cewa bangaren shari’ar kasar za su yi adalci tare da yin kira ga 'yan kasa da su rungumi zaman lafiya a yayin da ake ci gaba da zaman sauraron karar da suka shigar a gaban kotun.
Shi ma jagoran lauyoyi dake kare hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC, A.B Mahmud mai mukamin SAN, ya yi bayanin cewa kotu na da ikon ba da izinin a amince da bukatun jam’iyyar PDP da dan takararta na daukar zaman kotu kai tsaye a kafafen watsa labarai domin nunawa duniya.
To sai dai ya ce babu inda aka amince da hakan a baya a bisa doka yana mai cewa za su yi nazari da hukumar da suke karewa a gaban kotu don yin masaya a kan wannan batu.
Ita ma kotun koli ta dage zaman sauraron daukaka karar da jam’iyyar PDP ta shigar a kan hukumar INEC, jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, zuwa ranar 22 ga watan Mayu, sakamakon da wasu bayanai da hujojji Bola Tinubu da Kashim Shettima suka gabatarwa lauyoyin PDP a gaban kotun.
A bisa tsarin doka dai, jam’iyyar PDP na da kwanaki 3 don mayar da martani kan bayanan da Tinubu da Shettima suka shigar.
Saurari rahoton a sauti: