Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Zan Yi Wa Tattalin Arzikin Najeriya Garambawul" - Tinubu


Sabon Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Sabon Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Sabon shugaban Najeriya da ya harbi rantsuwar kama aiki a ranar Litinin 29 ga watan Mayu, Bola Ahemd Tinubu, ya sha alwashin yin gagarumin garambawul da ta da komadar tattalin arzikin kasar ta hanyoyi daban-daban.

ABUJA, NIGERIA - Hanyoyin sun hada da samar da ayyukan yi a fannin tattalin arzikin fasahar zamani, rage kudin ruwa da ake caji, samar da muhimman ayyuka, sake fasali a bangaren manufofin kudi da dai sauransu.

An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

Tinubu, ya bayyana hakan ne a yayin gabatar da jawabinsa bayan karbar rantsuwar kama aiki a dandalin Eagle square dake birnin tarayya Abuja.

“Za mu sake garambawul a fannin tattalin arziki ta hanyoyin karin samun kudadden shiga na GDP, samar da ayyukan yi, samar da wadataccen abinci da kuma kawo karshen talauci" in ji Tinubu.

Ya kara da cewa zai yi kwaskwarima ga tsarin kasafin kudin shekara-shekara na kasar tare da samar da wani tsari na daban wajen tabbatar da an farfado da masana’antun kasar rage dogaro da shigowa da kayayyaki cikin kasar da kuma samar da wutar lantarki ga kowa da kowa a farashi mai rahusa.

An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

‘Yan Najeriya da dama na bayyana ra'ayoyinsu kan jawabin na shugaba Bola Tinubu a game da yin garambawul ta fuskar tattalin arziki.

Masanin tattalin arziki, Malam Kasim Garba Kurfi ya ce alkawuran shugaban ta wannan fannin abubuwa ne da za su yiwu amma sai an tashi tsaye.

A na shi bangare, masanin tattalin arziki, Malam Yusha’u Aliyu ya bayyana cewa muddin gwamnati tana son ta taimaki tattalin arziki sai an tsaida hauhawar farashin kayayyaki.

An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
An Rantsar Da Bola Tinubu A Matsayin Shugaban Kasar Najeriya

Akasarin 'ya Najeriya na ganin cewa tabbas idan sabon shugaban ya aiwatar da abubuwan da ya ambata a kan lokaci za’a sami sauki, sai dai kuma aiwatarwa din ne za'a jira an ga yanayin kamun ludayinsa.

Masana tattalin arziki dai sun bayyana cewa akwai yiyuwar kudadden shigan GDP na Najeriya ya kai dala biliyan 454.05 nan da karshen shekarar 2023, kuma a bisa dogon zango, ana hasashen cewa GDP na Najeriya zai kai kusan dala biliyan 469.04 a shekarar 2024 da kuma dala biliyan 482.64 a shekarar 2025, bisa ga tsarin tattalin arzikin kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Halima AbdulRauf:

Tinubu Ya Ce Zai Yiwa Fannin Tattalin Arzikin Najeriya Garambawul.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:59 0:00

XS
SM
MD
LG