Kotun ta yi hakan ne don baiwa dukkan bangarorin da al’amarin ya shafa lokaci da zasu sami damar warware inda ake da takaddama a kan bukatu da takardun da za’a gabatar a zama na gaba.
A cikin karar mai lamba ta CA/PEPC/05/2023, jam’iyyar PDP da dan takararta Atiku Abubakar suna kalubalantar ayyana Bola Ahmed Tinubu a matsayin zababben shugaban kasa da hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya wato INEC ta yi a ranar 1 ga watan Maris na shekarar 2023 wato kwanaki hudu bayan gudanar da babban zaben 25 ga watan Febrairu.
Alkalin kotun mai tawagar manyan lauyoyi biyar, mai shari’a Haruna Tsammani ne ya dage sauraron karar zuwa ranar 18 ga watan Mayu domin ci gaba da zaman share fagge kafin a saurari ainihin karar da zai kaiga zartar da hukunci.
Lauyan wadanda suka shigar da kara, Cif Chris Uche, mai mukamin SAN, ya shaidawa kotun cewa dukkan bangarorin wato lauyoyin wadanda ake kara sun gana kuma sun amince da hanyoyin da za a bi wajen rage kananan ababen da ba’a bukata a yayin zaman kotun da ka iya kawo tasgaro domin ganin an karasa zaman sharar fagge a kan lokaci kafin sauraron ainihin karar da aka shigar.
Babban lauya mai mukamin SAN kuma daya daga cikin tawagar lauyoyin dake kare Bolą Tinubun a kotu, Dakta Hassan Liman, ya yi bayani a kan abun da ya wakana cikin kotun, yana mai cewa dukkan lauyoyin dake wakiltar wadanda suka gabkatar da kara da ma wandada ake kara sun yi magana kuma sun amince da a je a zauna a duba dukkan hujjojin da takardu da ake dasu don a gabatarwa kotu cikin sauki.
Wadanda aka jera a matsayin na 1 zuwa na 3 a cikin karar dake gaban kotun su ne INEC, Bola Tinubu, da kuma jam’iyyar APC wanda suka sami wakilcin lauyoyi masu mukamin SAN sama da 30.
Shi ma kakakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma daya daga cikin tawagar lauyoyin dake kare shi a gaban kotu, Daniel Bwala, ya ce har yanzu suna kan bakansu na cewa sune suka sami nasara a zaben na watan Febrairu kuma suna shirye su gabatarwa kotu hujjojinsu kań lamarin.
Daniel Bwala ya kuma ce zaman lafiya a cikin kasar na da mahimmanci a yayin da ake dakon hukuncin da kotun zata zartar a wannan shari’a.
Kazalika, da yake dage ci gaba da sauraren karar, Mai shari’a Tsammani ya yaba wa dukkan bangarorin da shari’ar ta shafa da suka bayar da hadin kai da amincewa da yadda zaman kotun ke tafiya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen kammala zaman da ake yi a kan lokaci.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman kotun na ranar Alhamis dai akwai wanda ya shigar da kara na 1, Atiku Abubakar, wanda a cikin takardar sa ta hadin gwiwa da jam’iyyar PDP mai lamba: CA/PEPC/05/2023, ya nemi a janye takardar shaidar lashe zabe da humumar INEC ta baiwa zababben shugaban kasa, Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki.
Saurari rahoton a sauti: