Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Musamman Ta Zabe Ta Fara Sauraren Kararrakin Da Aka Shigar Na Zaben Watan Febrairu


Kotun zaman kararraki a zaben shugaban kasa
Kotun zaman kararraki a zaben shugaban kasa

Kotun musamman ta sauraren kararrakin zaben shugaban kasar Najeriya da ke zama a Abuja ta fara shara Faggen zaman sauraren kararrakin zaben shugaban kasa da aka shigar a gabanta.

A yayyin zaman, ta saurara tare da nazari kan kararraki 3, inda kuma ta yi watsi da karar jam’iyyar Action Alliance, bayan da jam'iyyar ta nemi janye karar da ta sigar a gaban kotu tare da dage zaman kararrakin zuwa ranar Laraba 10 ga watan Mayu.

Jagora a zaman shari'ar kararrakin zaben shugaban kasa da ake yi a cikin babbar kotun daukaka kara ta Najeriya da ke Abuja, mai shari’a Haruna Simon Sammani ne ya zartar da hukuncin yin watsi da karar da jam’iyyar Action Alliance ta shigar, biyo bayan bukatar neman janye karar da lauya mai wakilyar jam’iyyar ya gabatar a gaban kotun a yau litinin.

Barrister Dauda AbdulMaleek Usman na daya daga cikin lauyoyin da suka wakilci jam’iyyar Action Alliance a gaban kotu inda ya ce dalilin da ya sanya suka janye karar su shi ne rashin mutunta hukuncin kananan kotu biyu da hukumar zabe ta yi bayan an rubuta mata wasika a kan shugaban jam’iyyar da kotu ta sani.

Daga bisani bayan amincewar dukkan wadanda ake kara a gaban kotu da bukatar jam’iyyar A.A din da suka hada da INEC, jam’iyyar APC da dai sauransu, mai shari’a Sammani ya zartar da hukuncin yin watsi da karar gabadaya.

Mai shari’a Haruna Simon Sammani da saura mambobin tawagarsa a wannan aikin sun saurarri bayanai daga bakin masu shigar da kara na biyu da na uku, wato Jam’iyyar APP da Leba party inda ake karar jam’iyyar APC, zababben shugaban kasa da mataimakinsa, hukumar INEC da dai sauransu.

Daga bisani an dage zaman sauraron bayanan share Fagge a kan shari’ar zuwa ranar Laraba 10 ga watan Mayu, kamar yadda jagoran lauyoyin da ke kare hukumar INEC, Abubakar Balarabe Mahmud ya yi bayani.

Shi ma jigo a jam’iyyar Leba party, Dr. Yunusa Tanko, yace janye karar da jam’iyyar AA ta yi bai sare musu gwiwa ba ganin dalilan da ya sa aka dauki mataki, yana mai cewa ya sami kwarin gwiwa a matakan da kotu ta dauka a yau da aka fara zaman saurarron kararrakin su, ganin yadda aka ba kowa damar gabatar da ababen da ake bukata kafin fara zama gadan-gadan.

Dukkan jagororin lauyoyin wadanda al’amarin kotun ya shafa dai sun sha alwashin baiwa kotu goyon bayan da ya kamata don gaggauta aikin sauraron kararrakin da zartar da hukunci daidai da doka.

A yanzu dai kotun ta dage sauraron bayanan shari’ar share fagge da bada amsoshi takanin dukkan wadanda al’amarin ya shafa a kararraki na 2 da uku zuwa ranar Laraba 10 ga watan Mayu, kuma za’a saurari bahasin shara fagge a cikin kararrakin da jam’iyyar PDP da APM suka shigar da ke matakin na 4 da 5 daga gobe talata 9 ga watan Mayu.

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:03 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG