Sabon Firayim Ministan Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ya ce tsaron lafiyar 'yan kasar na daga cikin manyan abubuwan da zai sa a gaba.
A wani lamari mai cike da tarihi, Kungiyar Kasuwanci ta Duniya ta zabi mace ta farko kuma 'yar Afirka ta farko da za ta jagoranci kungiyar.
Masu gabatar da kara a shari’ar tsige tsohon shugaban Amurka Donald Trump a Majalisar Dattawan kasar sun koma yau Alhamis don gabatar da hujjojin cewa Trump ne ya tunzura mummunan farmakin da aka kai kan ginin Majalisar a watan jiya.
Tawagar gwamnan jihar Babagana Umara Zulum ta yi mummunar hatsarin mota yayin da suke komowa Maiduguri inda mutane 3 suka rasa rayukansu.
Jami’an tsaron kasar Somaliya 12 ne aka kashe, wasu 2 kuma suka raunata a jiya Lahadi, biyo bayan fashewar wani abu a gefen titi a tsakiyar jihar Galmudug, a cewar mahukunta
An gudanar da zanga-zangar adawa da mulkin sojan Myanmar a rana ta uku a jere, yau Litinin, mako guda bayan da sojoji suka tsare Aung San Suu Kyi, da sauran shugabannin zababbiyar gwamnatin farar hula.
Shugaban Amurka Joe Biden, ya ce ba zai dage takunkumin tattalin arziki da aka kakabawa kasar Iran ba, har sai Tehran din ta rage yawan aikin bunkasa sanadarin Uranium din ta, kamar yadda aka cimma, a yarjejeniyar kasa-da-kasa ta 2015, wanda aka yi, don hanata hada makaman, na kare dagi.
Akalla mutane tara da suka hada da wani janar na soja sun mutu, wasu 15 kuma suka jikkata a wani harin da kungiyar Alshabab ta kai a wani otal a Moghadishu.
Sojojin Myammar sun kwace ikon kasar a yau Litinin karkashin dokar ta-baci da aka sanya na shekara guda, saboda rashin daukar mataki kan korafin da suka yi cewa an yi magudi a zaben da aka gudanar a watan Nuwamba.
Shugaban Amurka Joe Biden na shirin karbar bakuncin wasu sanatoci 10 ‘yan jam’iyyar Republican don tattaunawa yau Litinin game da wani sabon zagaye tallafin tattalin arzikin coronavirus.
Tsohon gwamnan jihar Imo Sanata Rochas Okorocha ya musanta zargin cewa ya fice daga jam'iyyar APC mai mulki kuma ya kafa wata sabuwar jam'iyya mai lakabin New Nigeria Movement.
Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ya kai 1,633 a ranar Asabar kadai a Najeriya a cewar hukumar NCDC mai sa ido akan cututtuka masu yaduwa.
Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya ce dukkan masu haddasa fitina a jihar sune za su sa kafar wando daya da su amma ba masu neman halal dinsu ba.
A ƙoƙarin da ta ke yi wajen farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa, gwamnatin Nijeriya ta ɓullo da tsare-tsare don bunƙasa ɓangaren noma da kuma inganta shi da nufin rage dogaron da ƙasar ke yi kan man fetur.
A yayin da ya rage ‘yan sa’oi kadan a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasar Nijer hade da na ‘yan majalisar dokoki, kungiyoyi masu zaman kansu na ci gaba da kara jan hankulan jama’a don ganin komai ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Kungiyoyin addinai biyu a Najeriya sun yi maraba da matakin da Amurka ta dauka na sanya Najeriya a rukunin kasashen da ake zargi da saba ‘yancin addini.
A ranar 28 ga watan Nuwamba ne aka tsare wata ma'aikaciyar Muryar Amurka tsawon sa’o’i 5 a Port Harcourt a lokacin da ta ke bakin aiki.
Gwamnatin Jihar Neja a Najeriya ta ce za ta ba da tallafi na musamman ga iyalan ‘yan banga da suka mutu a lokacin da suke yaki da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar. Daruruwan ‘yan banga ne dai ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla a sassa dabam-daban na jihar Neja.
Domin Kari