Daga cikin tsare-tsaren akwai samar da ingantaccen iri ga manoma, taki, da bayar da bashi da tallafi ga ƙananan manoma da Babban Bankin Nijeriya ke jagoranta.
Nura Lawan Daura, jami'i a ma’aikatar tallafa wa manoma ta Nijeriya da ake kira IFAD a takaice, ya ce hukumar na haɗa manoma da mutanen da za su riƙa sayen kayayyakinsu.
Ya kuma ce galibin mutanen da hukumar ta ke amfani da su an horar da su musamman akan noma na iri, kuma akwai mata da yawa da hukumar ta horar kan sarrafa rogo.
Shi ma Ibrahim Musa, manomi da ke wakiltar arewa maso yamma a majalisar tantance iri ta Nijeriya, ya ce gwamnati na ƙoƙari wajen tallafa wa manoman, sai dai ba sa gani a ƙasa. Ya kara da cewa waɗannan tallafe-tallafen da ake ta faɗa da ma’aikatan da aka ɗauki amana aka basu, duk a jarida ake gani kawai kuma su na wasa da hankalin ‘yan ƙasa da kuma kudurorin gwamnatin tarayya na bunƙasa tattalin arzikin ƙasa zuwa ga aikin noma.
Shugaban kungiyar manoman Nijeriya Kabir Ibrahim, ya ce abubuwan da ke addabarsu sun hada da rashin na’urorin noma, da masu bada shawarwari a bangaren noma, rashin kuɗi da rashin kasuwa. Manoma na buƙatar iri mai kyau, su na kuma bukatar tsaro wanda alhakin gwamnati ne ta samar da shi, a cewarsa.
Gwamnatin Najeriya dai ta bada tabbacin cewa buɗe kan iyaka da aka yi ba zai maida hannun agogo baya ba a nasarar da manoma su ka cimma ta wadatar abinci a cikin gida.
Saurari karin bayani cikin sauti: