Tsohon gwamnan kuma Sanata mai wakiltar Imo ta yamma, Rochas Okoracha, ya fito karara ya bayyana cewa har yanzu shi dan jam'iyyar APC mai mulki ne kuma bai kafa wata sabuwar jam'iyya ba. Wannan dai na zuwa ne bayan bayanan da ke yaduwa na cewa Sanatan ya kafa wata sabuwar jam'iyya mai suna "New Nigeria Movement" inda zai tsaya takarar shugaban kasa.
Sanatan ya musanta zargin ne a ta bakin wani mai magana da yawunsa Farfesa Nnamdi Obiriri, wanda ya fadi cewa ya san 'yan Najeriya daga jam'iyyu dabam-daban suna rokon Rochas ya tsaya takarar shugaban kasa kuma matsin lambar na da nauyi sosai, suna yin kiran ne a karkashin rukunin wasu talakawa da ake kira "New Nigeria Movement, a cewarsa.
Ya kara da cewa wadanda basu san asalin yadda lamarin ya ke ba ne suke cewa Rochas ya kafa sabuwar jam'iyya, amma hakan ba gaskiya ba ne har yanzu Rochas ya na jam'iyyar APC.
Wani mai fashin baki kan lamuran siyasa Malam Abdullahi Yayandi, ya ce irin wadannan kungiyoyin siyasar da ake kafawa suna neman a san da su ne ta yadda zasu iya juya akalar yadda lamuran siyasa ke tafiya.
Yayandi ya kuma ce yadda abubuwa ke tafiya yanzu ta yiwu su yi tasiri sosai, saboda idan aka yi la'akari za a ga cewa kusan magana ce ta jam'iyyu biyu, a saboda haka indan aka ga Rochas ya jawo jama'a sosai to ta yiwu PDP ta yi zawarcin sa duba da cewa akwai kurakurai da yawa a APC yanzu.
Saurari cikkaken rahaton Alphonsus Okoroigwe: