Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Jihar Neja Ta Ce Za Ta Tallafa Wa Iyalan 'Yan Banga Da Aka Kashe


Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello
Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello

Gwamnatin Jihar Neja a Najeriya ta ce za ta ba da tallafi na musamman ga iyalan ‘yan banga da suka mutu a lokacin da suke yaki da ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar. Daruruwan ‘yan banga ne dai ‘yan bindiga suka yi wa kisan gilla a sassa dabam-daban na jihar Neja.

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello, a lokacin da ya gana da wasu daruruwan ‘yan banga a karamar hukumar Kontagora, ya bayyana cewa ya zama dole a gode musu saboda aikin da su ke yi na tsare gidaje, da al’umma, su na kuma taimaka wa ‘yan sanda da sojoji. Ya kara da cewa duk abinda ya dace a yi don a taimaka musu da kayan aiki za a yi Insha Allahu,

"Akwai ‘yan uwanmu da yawa da suka rasa rayukansu, gwamnati za ta duba yadda za a taimaka wa iyalansu amma abinda ya fi muhimmanci a ciki shi ne, duk wanda ya rasa ransa, gwamnati za ta dauki nauyin kudin makarantar ‘yan’yansa," a cewar gwamnan.

Lamarin ‘yan bindiga a jihar Neja dai na ci gaba da kara ta’azzara, kamar yadda wani mazaunin karamar hukumar Mashegu ya shaida, ya na mai cewa 'yan bindiga sun kama wasu wurare a cikin jihar Neja sun kuma kori manoma da mazauna kauyukan.

Wannan al’amari dai ya sa a yanzu haka manyan jami’an gwamnatin jihar Neja yin damarar sa kayan 'yan banga domin tunkarar ‘yan bindigar. Kwamishinan ma’aikatar kula da harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkindaji na daya daga cikin waddanda suka saka kayan ‘yan bangar.

"Harkar tsaro aiki ne na duk wani mai hankali ba na ‘yan banga ba ne kadai. Ya kara da cewa idan kwamishina zai sa kayan 'yan banga don neman miyagu, to kai da ka ke gida me zai hana ka yi? a cewar Abdulmalik.

Daya daga cikin shugabannin ‘yan bangan Alhaji Aliyu Makiga, ya nuna gamsuwa da tallafin da gwamnatin ta ce za ta basu, ya kuma ce su na bukatar kayan aiki domin tunkarar wadannan ‘yan bindiga da ko a makon jiya sai da suka hallaka wasu sojojinn Najeriya guda shida tare da wasu ‘yan bangan guda biyu a jihar Neja.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00


Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG