Sanata Ali Ndume ya ce Kotu ba ta bashi damar ya kare kansa ba bayan da ta bada umurnin a tsare shi a gidan yari.
Fargabar yiwuwar barkewar yakin basasa na karuwa a kasar Habasha bayan da gwamnatin tarayyar kasar ta zafafa kai hare-hare a yankin Tigray.
A Bangaladash akalla mutane dubu hamsin suka fito kan titunan Dhaka, babban birnin kasar a yau Litinin, don nuna adawa da shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda ya kare sukar Musulunci a matsayin ‘yancin bayyana ra’ayi.
Ina-Za-Mu-Je-Matasa: A cikin shirin wanna makon za ku ji yadda ‘yanci da kalubalen da yara mata ke fuskanta a fadin duniya. Abun da ya hada da fyade, cin zarafin mata, rashin ilimi da dai makamatansu-Kashii na biyu.
Harbin masu zanga-zangar lumana a Lagos da wasu jami'an tsaro suka yi ya janyo suka sosai a ciki da wajen Najeriya.
Yanci da kalubalen da yara mata ke fuskanta a fadin duniya. Abun da hada da fyade, cin zarafin mata, rashin ilimi da dai makamatansu
Rana ta baci ma wasu miyagu su wajen 11, a daidai lokacin da su ke kan tsara wata ta'asa a karamar Hukumar Kurfi ta jihar Katsina a Najeriya.
Ga dukkan alamu akwai sauran rina a kaba, game da batun daure yara ana gallaza masu saboda wasu dalilai iri iri. Na baya bayan nan shi ne wani yaro dan kimanin skekaru 12 da aka daure jikin wani gungume ana gallaza masa a gidansu.
Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da yarjejeniyar gyara dangantaka tsakanin kasar da Hadaddiyar Daular Larabawa da ake kira UAE a takaice.
Kwamitin shari'a na Majalisar Dattawan Amurka ya fara zaman tantance Amy Coney Barrett wadda Shugaba Donald Trump ya zaba ta zama mai shari'a a kotun kolin Amurka.
Masana kimiyya a Australia sun gano cewa kwayar cutar coronavirus da ke haifar da COVID-19 za ta iya jure rayuwa akan wasu abubuwa har zuwa tsawon kwanaki 28.
Bayan dan tsaikon da aka samu da kuma jita-jita kan ko waye zai zama sabon sarkin Zazzau, yanzu wannan ya zama tarihi saboda an nada Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon sarkin Zazzau.
'Yan sa'o'i bayan nada Mai Martaba Sarkin Zazzau, ya yadda ya yi hira ta farko da Gidan Rediyon Muryar Amurka kan wasu muhimman abubuwa
A Najeriya, ra'ayoyin 'yan Majalisar dattawa sun rarrabu akan batun sake tsayawa takarar tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan, inda wasu ke cewa kundin tsarin mulki bai hana ba, wasu kuma ke cewa ya hana.
A jamhuriyar Nijer, dan takarar jam’iyar RANAA, Dr Hamidou Mamadou Abdou ya sha alwashin hukunta mahandama dukiyar jama’a idan ya ci zaben Shugaban kasa.
Fadan da ake yi tsakanin sojojin Armenia da Azerbaijan kan yankin Nagorno-Karabakh ya bazu har zuwa bakin iyakokin yankin da ake takaddama a kansa jiya Lahadi 4 ga watan Oktoba.
Mako guda bayan da mace-mace sakamakon coronavirus suka zarta miliyan 1, an samu sama da mutane miliyan 35 da suka kamu da COVID-19 a kasashen duniya, a cewar Cibiyar samar da bayanan Coronavirus ta Johns Hopkins.
Gwamnati ta kebe wurin bada tarbiyya wa kangararrun yara, da basu kai shekaru goma sha takwas ba, don kaucewa take-taken da suka dauka na zamewa matsala a tsakanin al’umma.
Shugaban kwamitin Shugaban Nigeria Mai binciken badakalar da ake zargin Mustafa Ibrahim Magu ya tafka a hukamar yaki da cin hanci da rashawa, Justice Ayo Salami ya karyata labarin da lauyoyin Magu suka yada na cewar wai yayi nadamar kar’bar aikin.
Domin Kari