A jiya Lahadi wata mota dauke da Bam ta tarwatse a kusa da wani Otel a Magadishu, babban birnin kasar Somalia. Bayan tashin bom din, harbe-harbe sun biyo baya a tsakanin ‘yan ta’adan da ‘yan sanda.
Kungiyar ‘yan ta’adda ta Al-shabab ta dauki alhakin kai wannan harin.
Wani da ya shaida lamarin, ya ce bom din ya tashi a jiya Lahadi a kusa da Otel Afrik, yankin mai cike da shingayen bincike na jami’an tsaro akan hanyar zuwa tashar jirgin sama da ke Magadishu.
‘Yan sanda sun tabbatar da cewar ‘yan kungiyar Al-shabab sun abka cikin Otel din, amma sun samu damar kubutar da mutanen da ke ciki, wanda suka hada da tsohon ministan tsaron na Somali Yusuf Siad Inndha-Adde.
Wakilin Muryar Amurka Abdikafi Yusuf Aden, na daya daga cikin wadanda abun ya rutsa da su a cikin Otel din, amma dai ya kubuta.
Aden, ya ce bayan tashin bom din hayaki ya turnike, jama’a sun yi ta fadowa daga saman bene, don tsira da rayukansu.