Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan Jihar Oyo Ya Ce Ba Sa Adawa Da Fulani Makiyaya


Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde ya ce dukkan masu haddasa fitina a jihar sune za su sa kafar wando daya da su amma ba masu neman halal dinsu ba.

Gwamnan jihar Oyo Seyi Makinde, ya fadi cewa ba sa adawa da fulani makiyaya muddin masu neman halal dinsu ne, amma suna adawa da masu aikata laifuffuka kamar fyade, fashi da makami, garkuwa da mutane da dai sauransu, ba tare da la'akari da kabila, ko addini ba.

Gwamnan ya kuma ce dukkan masu haddasa fadan jinsi, za a kama su a hukunta su.

Da suke maida martani game da kalaman gwamnan, shugabannin Hausa/Fulani kamar Ibrahim Jijji, shugaban kungiyar Myetti Allah ta jihar Oyo, ya ce sun ji dadin abinda gwamnan ya fada. Ya kuma ce dama sun tabbata zai yi musu adalci, mussaman masu neman halal.

Jijji ya kuma ce su ma su na adawa da masu aikata manyan laifuffuka, don a cewarsa zaman lafiya suke nema, amma kuma su na fatan gwamnan zai neme su ya tattauna da su akan duk wani abu da za a yi da zai shafesu bisa ga tsarin doka a kuma yi binciken lamarin.

Shi ma Ado Suleiman sarkin Hausawan yankin, ya ce maganar da gwamnan ya yi magana ce ta gaskiya, ya kara da cewa bai dace a ce a kullum bafulatane ne kadai a ke kira barawo ba.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG