Sojojin sun bada sanarwar ne a tashar talabijin sojoji ta Myawaddy inda suka ce za a yi zabe ya zuwa karshen shekara guda, inda sojoji za su mika mulki ga wanda ya yi nasara.
Wannan yunkuri ya zo ne sa’o’i bayan da aka tsare shugabar Myammar, Aung San Suu Kyi, da wasu jami’ai daga jam’iyya mai mulki ta National League for Democracy.
Kakakin NLD, Myo Nyunt ya ce Shugaba Win Myint yana cikin wadanda aka tsare da safiyar yau Litinin.
“A iya sanin mu, Sojojin Burmi sun kama dukan muhiman mutane, don haka yanzu muna iya cewa wannan juyin Mulki ne."