Grace Alheri Abdu ta kai ziyarar aiki a Oyigbo ne, wani gari da ke kusa da Port Harcourt babban birnin jihar Rivers, don samun bayanai game da zanga-zangar da aka yi a Najeriya ta kuma yi hira da masu shaguna a wurin da iyalan da tashin hankalin ya shafa.
Akan hanyarta ta komawa, ta bi ta wani ofishin ‘yan sanda da masu zanga-zanga suka kona kurmus. Abdu ta gabatar da kanta ga wani jami'in tsaro a wurin, kuma ta na dauke da katin shaidar aikinta wanda ya nuna ita 'yar jarida ce.
Amma a lokacin da ta wuce ginin don daukar hotuna, wani soja ya tsayar da ita ya bukaci sanin ko ita wacece da kuma inda za ta.
Abdu ta ce sai sojan ya wurgar da wayarta kasa, ya kwace na’urar maganar da ta rike sannan ya kuma yi mata barazana. Wasu sojoji kusan su 10 suka tsareta tare da barazanar za su yi mata duka, bisa zargin ita “makiyar kasar ce.”
Kakakin rundunar sojan Najeriya Kanal Sagir Musa, ya tura Muryar Amurka ta yi magana da mataimakinsa don ya yi bayani kan lamarin. Mataimakin bai amsa kiran waya da sakon kar ta kwana da aka aika masa ba. Haka kuma Muryar Amurka ba ta samu amsar sakon email da ta tura shafukan sada zumuntar rundunar ba.
Wani wanda ya shaida lamarin ne ya tura wa kungiyar ‘yan jaridar Afrika ta yamma bayanin duk abinda ya gani ya kuma bukaci su tuntubi ofishin jakadancin Amurka, don a kai wa ‘yar jaridar dauki.