Masu gabatar da karar, wadanda suka hada da yan majalisar wakilai na jam’iyyar Democrat, sun nuna wa sanatocin da ke shari’ar wani bidiyo wanda ba a taba gani ba a baya, game da tashin hankalin a jiya Laraba.
Bidiyon ya nuna daruruwan masu tayar da kayar baya - magoya bayan Trump, da tsohon shugaban ya bukacisu su je ginin majalisar su yi kokarin hana zartar da sakamakon zaben da ya sha kaye– inda suka kutsa cikin ginin har ma cikin dakunan ‘yan majalisun. Wasu daga cikin masu tarzomar sun bincike takardun da 'yan majalisar suka bari a kokarin gudun tsira da ransu.
Haka kuma wasu daga cikin masu tarzomar, da bidiyon na ranar 6 ga Janairu ya nuna, da karfi sun yi ta fadin suna kokarin gano tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Mike Pence don rataye shi saboda ya ki amincewa da bukatar Trump ta neman hana a zartar da sakamakon wakilan Zabe, ta yadda Trump da Pence zasu ci gaba da kasancewa kan mulki wani wa'adin shekaru hudu.