A Najeriya, kwararru a fanin man fetur sun tafka mahawara akan komitin da Shugaban kasa Mohammadu Buhari ya nada, wanda zai yi duba ga yadda dokar sake fasalin masana'antar man fetur ta kasa, za ta yi wa yan kasar amfani ko akasin haka.
Najeriya ta fara kashi na biyu na allurar rigakafin cutar coronavirus a kasar baki daya a yayin da ake ci gaba da samun karuwar masu kamuwa da nau’in Delta na cutar.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun ayyana zaman makoki na kwanaki 2 daga yau laraba sakamakon kisan da ‘yan ta’adda suka yi wa fararen hula kimanin 37 a kauyen Darey Dey na gundumar Banibangou jihar Tilabery a ranar litinin da ta gabata.
Ma'aikatar lafiya ta Uganda ta tabbatar da barkewar cutar shan inna a cikin kasar bayan samfuran da aka tattara daga ruwan najasa a Bugolobi da Lubigi.
‘Yan ta’adda na ci gaba da karkashe fararen hula a yankin Tilabery na jamhuriyar Nijer inda ko a jiya litinin ma wasu gwamman fararen hula akasarinsu mata da yara kanana suka gamu da ajalinsu sakamakon harin da ya rutsa da su a kauyen Darey Dey na gundumar Banibangou.
Ofishin Kididdiga ta kasa ta fitar da rahoto da ke cewa Najeriya ta sami kudi har Naira biliyan 512 da yan kai a cikin wattani uku kachal, sai ya rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa,Najeriya ita ce kasa ta 5 a ayarin kasashen da ke yawan cin bashi.
Yajin aikin Likitocin Najeriya ya tarwatsa tsarin kiwon lafiya a yayin da ake fama da annobar Covid-19.
A ragar Alhamis ne Najeriya ta karbi allura riga-kafin cutar korona nau’in J&J kimanin dubu 176,000.
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ya mamaye kasar Nijer da ke Yammacin Afirka tun daga watan Yuni ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 55 sannan mutane 53,000 suka rasa matsugunansu, bisa ga cewar hukumomi.
Kamfanin Royal Dutch Shell na Najeriya ya amince ya biya al'ummar a kasar da ke Yammacin Afirka sama da dala miliyan 110 don warware daddaden takaddamar kan malalar mai da ta faru sama da shekaru 50 da suka gabata.
Ma’aikatar harkokin wajen Indonesia ta bayyana nadamar ta bayan da jami’an shige da fice a Jakarta suka tsare wani babban jami’in diflomasiyya na Najeriya karfi da yaji, lamarin da ya sa gwamnati ta kira jakadanta da ke Abuja don tuntuba.
Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a jiya talata dadare a birnin Yamai ya hadddasa mutuwar mutane da dama.
Gwamnatin tarayya a ranar Laraba ta ce Twitter ta amince ta bude ofishinta a Najeriya a shekarar 2022.
Gwamna Andrew Cuomo ya sanar da cewa zai ajiye aiki cikin makonni biyu masu zuwa biyo bayan zargin shi da ake yi da cin zarafin mata.
Tun da farko dai an shirya fara gudanar da allurar rigakafin ne a yau Talata 10 ga watan Agusta sai aka dage domin baiwa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC da sauran hukumomin lafiya damar gudanar da bincike domin tabbatar da ingancin allurar.
A Jamhuriyar Nijar 'yan sanda sun kama wasu gomnan dalibai a birnin Yamai saboda zarginsu da yunkurin sata a jarabawar BAC ta ajin karshen kammala makarantun share shiga jami'a da aka gudanar a makon jiya a fadin kasar.
An kwantar da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma a asibiti, wanda aka daure saboda raina kotu a watan da ya gabata,asa da mako guda kafin a gurfanar da shi a gaban kotu don shari’ar cin hanci da rashawa.
Akalla mutane 30 ne, ciki har da sojoji, 'yan tawayen jihadi suka kashe a arewacin Burkina Faso, in ji gwamnatin kasar.
Kwararru a fanin tattalin arziki da wasu yan kasa na tafka mahawara akan wasu makudan kudaden Da Bankin lamuni na Duniya IMF ya zuba wa Najeriya a ssusun sa na Kasashen waje har dalar Amurka biliyan 3.35.
A Najeriya an gudanar da wani gagarumin taro kan matsalolin tsaro da nufin yin bita kan yakin basasar kasar na shekaru uku don ganin Irin darussan da za a iya dauka.
Domin Kari