Shugabar Hukumar Raya Kasashe Masu Tasowa ta Amurka Samantha Power na shirin ganawa yau Laraba tare da jami’ai a kasar Habasha yayin da Amurka ta yi kira da gwamnati da ta bada dama a kai kayan agaji zuwa yankin Tigray.
Hukumomi a Kamaru sun ce suna samun karuwar mayakan Boko Haram da ke mika kansu a wata cibiyar kwance damarar makamai da ke kan iyakar arewancin kasar da Najeriya.
A Najeriya, ana ci gaba da samun wadanda cutar kwalara ke harba a 'yan makonnin nan, mafi akasari a arewacin kasar yayin kuma da ake fama da cutar COVID-19 a gefe guda.
An kashe mutane da dama a wani rikici tsakanin Irigwe da Fulani a karamar hukumar Bassa da ke jihar Filato.
Ma’aikatar tsaron Jamhuriyar Nijar ta ba da sanarwar mutuwar sojojin kasar kimanin 15 sannan wasu 6 suka yi batan dabo yayin da 7 suka ji rauni.
Jami’ai a kasar Kamaru sun ce da alama mayakan Boko Haram sun sauya dabarun su, inda a yanzu suke kai hari kawai kan sojojin da wuraren gwamnati a kokarin da su ke yi na janyo daukan wasu da dama.
Hukumomin jamhuriyar Nijer sun kama wasu mutanen da ake zargi da fitar da dubban miliyoyin cfa daga asusun bital malin kasar ta barauniyar hanya lamarin da wasu ke ganin za ta yiwu allura ta tono galma idan aka zurfafa binciken.
A Jamhuriyar Nijer yau ake bukin raya ranar dimokradiya wace ta samo asali daga babban taron mahawarar kasa na ranar 29 ga watan yulin 1991 wanda ya kawo karshen mulkin soja na tsawon shekaru 16.
Mayakan kungiyar Boko Haram sun kashe sojojin Kamaru biyar da wani farar hula a wani hari da suka kai a yankin arewa mai nisa na kasar, in ji ma’aikatar tsaron ranar Talata.
Babbar kotun shari’ar musulinci dake Kofar kudu a tsakiyar birnin Kano ta umarci a ci gaba da tsare Malam Abaduljabbar Nasiru Kabara a gidan gyaran hali zuwa ranar 18 ga watan Agusta mai kamawa.
A Jamhuriyar Nijar jam’iyun hamayya sun gudanar da taron gangami da nufin jaddadawa ‘yan kasar cewa suna nan kan bakansu na masu adawa da gwamnatin shugaba Mohamed Bazoum wace suke yiwa kallon mara halarci.
Mahukuntan Kamaru na kira ga jama'a da su yi allurar rigakafin COVID-19, biyo bayan gudummawar da Amurka ta bayar a ranar Litinin na allurai 300,000 na Johnson & Johnson.
Bayanai daga kungiyar likitocin Ghana sun tabbatar cewa, da kasar ta fada cikin barkewar annobar COVID-19 karo na uku kana binciken ya tabbatar da nau’in cutar ta Delta na barna a kasar.
Domin Kari