Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnan New York Andrew Cuomo Ya Yi Murabus Kan Zargin Cin Zarafin Mata


Andrew Cuomo
Andrew Cuomo

Gwamna Andrew Cuomo ya sanar da cewa zai ajiye aiki cikin makonni biyu masu zuwa biyo bayan zargin shi da ake yi da cin zarafin mata.

Wannan na zuwa ne bayan da aka ja tsawon shekara guda ana yaba masa sabili da bada cikakkun bayanai yau da kullun da kyakkyawan jagoranci yayinda a ke ta fama da annobar COVID-19.

Cuomo a cikin faifan bidiyo ya ce "Ganin yanayin yadda abubbuwa ke gudana, ina ganin abun da ya dace da zan iya taimakawa da shi yanzu shine in ja gefe guda in bar gwamnati ta dawo kan mulki,"

An sanar da hukuncin gwamnan wanda yayi wa'adi uku a matsayin wani ci gaba da aka samu a majalisar don tsige shi. Hakan ya faru ne bayan da babban lauyan New York ya fitar da sakamakon wani bincike da ya gano Cuomo ya ci zarafin akalla mata 11.

Masu bincike sun ce ya yi wa mata sumba da ba a so, ya murza jikinsu in da bai dace ba, yayi maganganu da basu dace ba game da sassan jikinsu da kuma rayuwar jima'insu; abun da ya haifar da yanayin aiki "cike da tsoro da tsoratarwa."

Kathy Hochul, mai shekaru 62 da haihuwa kuma ‘yar majalisar wakilai daga yankin Buffalo ce za ta maye gurbinsa, ta zama gwamnan jihar ta 57 kuma mace ta farko da za ta rike wannan mukami.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG