Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’ai Sun Ce 'Yan Tawayen Jihadi Sun Kashe Mutane 30 A Arewacin Burkina Faso


Akalla mutane 30 ne, ciki har da sojoji, 'yan tawayen jihadi suka kashe a arewacin Burkina Faso, in ji gwamnatin kasar.

'Yan ta'adda sun kashe fararen hula 11, sojoji 15, da mayaƙan tsaro guda huɗu a wasu ƙauyuka da ke wajen garin Markoye a lardin Oudalan kusa da kan iyaka da Nijar a ranar Laraba, in ji Aime Barthelemy Simpore, mataimakin ministan tsaro a cikin wata sanarwa.

An kashe fararen hular da tsakar rana sannan aka yi wa sojoji da masu aikin sa kai kwanton bauna sa'oi hudu bayan an kebe su don tabbatar da tsaro a yankin, in ji gwamnati. Akalla 'yan tawayen jihadi 10 aka kashe, kuma sojojin sun tabbatar da tsaro a yankin, tare da yin sintiri ta sama da ta kasa.

Garin Gorom Gorom, kusan kilomita 40 (Mar mil 25) daga Markoye, ya cika da mutanen da ke tserewa harin, sakamakon fargabar tashin hankalin na iya yaduwa, kamar yadda wani ma'aikacin agaji a yankin ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press. Ya dage kan kada a sakaya sunansa don kare lafiyarsa.

Tashe-tashen hankula da ake danganta ta da al-Qaida na karuwa a Burkina Faso, inda suka kashe dubban mutane tare da raba mutane miliyan 1.3 da muhallansu. A watan Yuni, akalla ‘yan sanda 11 aka kashe lokacin da aka yi musu kwanton bauna a arewa kuma a farkon wannan watan an kuma kashe fararen hula akalla 160 a yankin Sahel. Wannan shine tashin hankali mafi muni cikin shekaru.

Rikicin na wannan makon ya zo ne bayan wani mummunan hari a makwabciyar Nijar da ke kan iyaka da Burkina Faso, kasa da mako guda da ya gabata, inda masu jihadin suka kashe akalla mutane 19, 18 daga cikinsu sojoji ne.

Zai yi wuya a shawo kan tashe-tashen hankulan na masu tsattsauran ra'ayi, a cewar masu sharhi kan rikice-rikice.

XS
SM
MD
LG