Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

COVID-19: Najeriya Na Shirin Gudanar Da Allurar Riga-kafin Moderna


Allurar riga-kafin lutar COVID-19 ta Moderna
Allurar riga-kafin lutar COVID-19 ta Moderna

Tun da farko dai an shirya fara gudanar da allurar rigakafin ne a yau Talata 10 ga watan Agusta sai aka dage domin baiwa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC da sauran hukumomin lafiya damar gudanar da bincike domin tabbatar da ingancin allurar.

Shugaban hukumar ya ce ana tunkarar kashi na biyu na rigakafin ne bayan kammala kashi na farko sun kuma dauka kwararan matakan tabbatar da cewa ba allurar rigakafin Astrazanneca ko daya data rage ba’ayi amfani da ita ba.

Dr Faisal ya kara da cewa Najeriya za ta karbi allurar J&J kimanin dubu dari da saba’in da shida (176,000) da za’a yi wa mutanen dake zaune a yankunan dake da wahalar isa duba da cewa idan akayi sau daya ya wadatar sabanin sauran alluran da ake yi sau biyu.

Faisal kuma kara da cewa kasar zata karbi alluran AstraZanneca dubu dari bakwai (700,000) don gudanar dasu ga wadanda suka karbi kashi na farko.

A nasa bangaren daraktan tsare-tsare, bincike da kididdiga na hukumar kuka lafiya matakin farko ta kasa Dr. Abdullahi Bulama Garba ya bayyana makomar mata masu juna biyu game da allurar rigakafin korona inda ya bayyana cewa a halin yanzu basa cvikin wadanda zasu karbi allurar.

Da take gabatar da jawabi a wajen taron, shugabar hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya Farfesa Mojisola Adeyeye ta tace a halin da ake ciki yanzu hukumar ta gama gudanar da duk wani shiri daya dace game da allurar ta moderna ta kuma kara tabbatar da ingancin ta.

Hakan na zuwa ne jim kadan bayan da kwamitin da Shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya kafa don yaki da annobar cutar korona ya fitar da sanarwa ta hannun daraktan yada labarai na kwamitin Mista Willie Bassey cewa an dage fara aikin gudanar da rigakafin.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

XS
SM
MD
LG