Wasu na ganin alheri ne ga kasa amma wasu na cewa wata hanya ce ta kara ruguza kasar da bashi.
Wanan hukunci da bankin bada lamuni na duniya ya dauka na kara habaka asusun da Najeriya ke ajiyewa a waje da dalar Amurka biliyan 3.35 abu ne da Shugabar bankin Kristialina Georgieva ta ce kudi ne da zai amfanar wa Najeriya bukatu na dogo lokaci wajen gina wa kasar karfin gwiwa a ha6aka tattalin arzikin ta, a fanin shawo kan tasirin da cutar korona ta yi wa tattalin arzikin kasar, amma kwararre a fanin nazarin zamantakewan kasashe da kuma siyasar kasa da kasa Abubakar Aliyu Umar ya ce wannan alamu ne na yaudarar Najeriya domin ta cigaba da karban bashi akai akai.
Abubakar Umar ya ce dama Najeriya ta riga ta ci bashi da yayi mata katutu kuma ba a ma san me aka yi da kudaden ba, saboda haka bamu da bukatar lamuni daga waurin kowa indai ba hikimaba ce na bautar da kasar.
To sai dai ga masanin kimiyar tattalin arziki na kasa da kasa Shu'aibu Idris Mikati, wannan wani yunkuri ne da bankin bada lamuni kan yi wa mambobinta da ke fuskantar nakasa a fanin tattalin arzikin ta kamar yadda Najeriya ta tsinci kanta a ciki a wannan lokaci na annobar cutar Korona.
Idris Mikati ya ce Najeriya tana cikin kasashen da IMF ke mutuntawa da kuma ganin kimar ta shi ya sa ma har za a sa ta a ayarin wadanda bankin ke yi wa lamuni.
Mikati ya kara jaddada cewa alamu ne na tallafawa wa Najeriya ta dogaro da kanta na lokaci mai tsawo kuma ba wai bashin tsabar kudi ne za a ba ta ba,bankin yana iya tsayawa a bayan Najeriya a duk lokacin da ta ke bukatar wani abu daga kowacce kasa a duniya.
Sanarwar da Shugabar bankin Kristialina Geirgieva ta fitar na nuni da cewa wannan mataki ne da bankin zai cigaba da dauka domin bunkasa arzikin kasashen da ke mambobin bankin dominsu samu cigaba mai dorewa.
Saurari cikakken rahoton a cikin sauti: