Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AFIRKA TA KUDU: An Kwantar Da Zuma A Asibiti Gabanin A Gurfanar Da Shi A Kotu


An kwantar da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Jacob Zuma a asibiti, wanda aka daure saboda raina kotu a watan da ya gabata,asa da mako guda kafin a gurfanar da shi a gaban kotu don shari’ar cin hanci da rashawa.

Sanarwar ta ce Ma'aikatar Kula da Ayyukan "za ta iya tabbatar da cewa a yau 6 ga watan Agusta 2021 aka kwantar da tsohon shugaban kasar Jacob Zuma a wani asibitin kasar waje domin duba lafiyarsa."

Zuma, mai shekaru 79, na shirin halartar ci gaba da shari'arsa kan cin hanci da rashawa da aka dade ana yi a ranar 10 ga watan Agusta.

Sauraron zai kunshi rokon da aka yi na nema a sauke tuhume -tuhume 16 na zamba, sata da cin hanci da rashawa da ake yi masa dangane da siyan jiragen yaki, jiragen ruwa na sintiri da kayan aiki daga kamfanonin makamai na Turai guda biyar lokacin yana mataimakin shugaban kasa.

Ana tuhumar sa da karbar cin hanci daga ɗaya daga cikin kamfanonin, babban hafsan tsaron Faransa Thales, wanda ake tuhuma da almundahana da halatta kuɗi.

An sha dage shari'ar sama da shekaru goma, lamarin da ya haifar da zargin dabaru na jinkiri.

Daure shi ya haifar da tashe-tashen hankali, sace-sace da barnar dukiyoyin a garinsa da ke lardin KwaZulu-Natal a babban birnin Johannesburg.

XS
SM
MD
LG