Fiye da gidaje 4,800 ne ambaliyar ruwa ko zaftarewar kasa ta lalata, kuma an yi asarar shanu kusan 900, in ji Kanal Bako Boubacar, shugaban hukumar kare fararen hula a gidan rediyon gwamnati.
Yankunan da abin ya fi kamari su ne Maradi a kudu maso gabas, Agadez a hamadar arewa da Yamai babban birnin kasar, inda 16 suka mutu.
Jamhuriyar Nijar, matalauciyar kasa ce mara ruwa a yankin Sahel, da ke fama da matsanancin ambaliyar ruwa. Lokacin damina bashi da tsawo, kuma yawanci yana gudana ne daga Yuni zuwa Agusta ko Satumba, kodayake a cikin 'yan shekarun nan yayi ƙarfi sosai.
A shekarar da ta gabata, ambaliyar ruwa ta yi sanadiyyar asarar rayuka 73 abinda ya haddasa rikicin jinkai inda mutane miliyan 2.2 ke bukatar taimako, a cewar Majalisar Dinkin Duniya. A 2019, 57 sun mutu.
Adadin wadanda suka mutu daga daminar bana, wanda aka bayar a ranar 31 ga watan Yuli, ya kai 35 sannan mutane 26,532 sun rasa matsuguninsu.