Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shell Za Ta Biya Diyyar Miliyan $110 Ga Al'ummar Malalar Man Najeriya Ta 1970 


Kamfanin Royal Dutch Shell na Najeriya ya amince ya biya al'ummar a kasar da ke Yammacin Afirka sama da dala miliyan 110 don warware daddaden takaddamar kan malalar mai da ta faru sama da shekaru 50 da suka gabata.

Lauyan da ke wakiltar al’ummomin Ejama-Ebubu a jihar Ribas, Lucius Nwosu ne, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na AFP kan wannan matakin.

Ya kara da cewa "Wannan shawarar ta biyo bayan korafin wannan al'umma wajen samun adalci."

Babban kamfanin zai biya mutanen Ejama-Ebubu diyyar dala miliyan 110.9 don kawo karshen shari'ar da aka fara a shekarar 1991, a cewar Nwosu.

Kamfanin Shell ya tunkari wata kotu a Abuja, babban birnin Najeriya, ranar Laraba don bayyana matakin, in ji shi.

Asalin korafin da al'umma ke yi wa kamfanin na Shell ya fara ne danagne da fashewar bututun kamfanin a shekarar 1970. Kamfanin Shell ya ce wasu ne suka yi sandiyar lalacewar muhallin a lokacin yakin basasa da ke ta'azzara a lokacin.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG