Wakilan Kungiyoyin Lafiya da suka hada hukumar lafiya ta duniya (WHO), hukumar lafiya matakin farko ta kasa (NPHCDA), Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF), Hukumar kare yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) da kuma kungiyar tarayyar Afirka (AU) sun shaida zuwan allurar ta J&J.
An sayo alluran ne ta hannun kungiyar tarayyar Afirka kuma wannan ne sahun farko nau'in J&J da aka fara karba a Najeriya.
Ana sa ran karbar wasu alluran kimanin sama da miliyan daya a cikin watan nan na Agusta.
Za’a fara fara aikin gudanar da allurar ne a ranar litinin 16 ga watan nan da muke ciki a cibiyar kiwon lafiya ta Abuja sannan a fara a sauran jihohin Najeriya.
Da yake jawabi a wajen taron manema labarai na ministoci da ake gudanarwa mako mako a fadar gwamnatin tarayya, ministan lafiya Dr. Osagie Ehanire yace gwamnati zata rika sayan alluran rigakafin korona ba tare da dogaro ga wadanda kasashe ke bata ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: