Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Ta Hallaka Mutum 5 A Birnin Yamai


Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu yankunan Nijar
Yadda ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu yankunan Nijar

Ruwan sama da aka tafka kamar da bakin kwarya a jiya talata dadare a birnin Yamai ya hadddasa mutuwar mutane da dama.

Sanadiyar ambaliyar ta haifar da rugurgujewar gidaje masu tarin yawa a wasu angwanni inda a yanzu haka wadanda abin ya shafa ke ci gaba da kwashe dan abinda ya yi saura domin zuwa neman mafaka.

Sama da milimita 100 na ruwan sama ne aka kyasta ce sun sauka a tsawon sa’oi 3 kacal a jiya dadare a birnin Yamai a wani lokacin da dama kasa ta riga ta jika sakamakon ruwan da ya tafka a cikin watan nan na Agusta.

Wasu yankunan Nijar da ambaliyar ruwa ta yi ta'adi
Wasu yankunan Nijar da ambaliyar ruwa ta yi ta'adi

“A angwanni Gabagoura dake shiyyar Yamai ta 1, jama’a ba ta rumtsa ba sanadiyar wannan al’amari” a cewar Ismael Idrissa.

Shi ma Hama Djibo wanda ruwa ya shafe gidansa da na wasu dangiinsa yace ya ga abin al’ajabi.

Balkissa wace ita da ‘yayanta suka sami mafaka a masallacin juma’a na Gbagoura na cewa ruwan ya wuce da komai na dakinta.

Domin jajantawa mutanen da abin ya rutsa da su wasu mazaunan Yamai sun leka a wannan wuri.

“Fiye da kashi 80 daga cikin 100 na gidaje ne suka ruguje a wannan angwanni sakamakon ruwan na jiya” inji Mai angwanni, Adamou Saley. Inda ya kara da cewa idan an dauki mataki, da hakan ba za ta faru ba.

Ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu yankunan Nijar
Ambaliyar ruwa ta yi barna a wasu yankunan Nijar

Magajin garin Yamai shiyya ta 1 Hamidou Abdou, yace ruwan da aka tafka a jiya daddare ya haddasa ambaliya a angwanni da dama inda a yanzu haka ake ci gaba da tattara bayanai. Haka kuma ya tabbatar da mutuwar mutun 1 a Gabagoura 4 a angwanni Yantala ta kasa.

A makon jiya hukumomin Nijer sun bayyana cewa mutane a kalla 40 ne suka rasu a fadin kasar sanadiyar ambaliyar ruwa a bana yayinda gidaje fiye da 25000 suka ruguje.

Saurari cikakkeen rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG